An yi wa daliba mai neman shiga jami’a fyade an kashe ta

An kama matashi kan zargin fyade da kisan budurwa mai neman shiga jami’a

An yi wa daliba mai neman shiga jami’a fyade an kashe ta

Gawa

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi fyade ga wata daliba da ke neman gurbin shiga manyan makarantu sannan suka kashe ta.

Shaidu sun ce an kai farmaki ne a gidan su dalibar aka yi mata fyade, sannan aka hallaka ta, a yankin Bosero da ke Karamar Hukumar Odeda ta Jihar Ogun.

Kakakin ’yan sandan jihar, Omolola Odutola, ya ce an tsinci gawar dalibar mai suna Temitope Elemide, da yanka a sassan jikinta da kuma kanta.

Wani shaida ya ce dalibar ta gamu da wannan mummunan ƙaddara ce a yayin da take shirye-shiryen zana jarabawar shiga manyan makarantu (UTME).

’Yan sanda sun ce suna tsare da saurayin budurwar bisa zargin sa da hannu, saboda a yayin bincike an kama shi yana fitowa daga cikin jeji.

Shugaban karamar hukumar,  Folashade Adeyemo, ya yi kira ga ’yan sanda da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da an hukunta duk masu hannu a wannan aika-aika.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda