An yi wa gwamnan Taraba ihun ‘ba mu so’ a wurin taro

Matasa da mata da kananan yara sun yi wa gwamnan Taraba ihun ‘ba ma so’ a gaban uban gidansa.

An yi wa gwamnan Taraba ihun ‘ba mu so’ a wurin taro

Gwamnan Taraba Darius Ishaku

Matasan Taraba sun yi wa Gwamna Darius Ishaku ihu a wurin taron mika sandar sarauta ga basaraken Donga da ke jihar, Ambasada Salvala Varzoa Shimbura.

Matasan yankin Kudancin jihar sun yi wa gamnan ihu ne a ranar Alhamsi, bayan ya halarci taron a matsayin babban bako na musmman, kuma a gaban uban gidansa, Janar TY Danjuma.

Aminiya ta gano yawancin matasan sun hada da ’yan jam’iyyarsa da PDP da kuma jam’iyyar adawa ta APC, inda suka rika la’antarsa, sun ihu suna, “Ba mu so, ba mu so.”

Hakan kuwa ta faru ne a yayin da ake tsaka da taron, a lokacin da Gwamna Darius ya mike domin kai gaisuwar ban girma ga Janar TY Danjuma.

A nan ne wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da matasa da mata da kananan yaran suka fara ihu cewa “ba mu so, bamu so.”

Wata majiya ta ce tun kafin taron wasu jami’an gwamnatin jihar suka je yankin suna raba wa mutane kudade, domin lallashin matasan yankin.

Sai dai Aminiya ta tuntunbi kakakin Gwamna Darius Ishaku, Mista Bala DanAbu, kuma ya musanta cewa jama’a sun yi wa gwamnan ihu a bikin mika sandar sarautar da ta gudana a Donga.

A cewar Bala DanAbu, “Babu wanda ya yi wa Gwamna Darius Ishaku ihu, sai ma yabon da ya samu saboda cigaban da ya kawo wa jihar.”

Ya yi zargin cewa, ”Magoya bayan Sanata Emmanuel Bwacha suka nemi su mayar da taron na siyasa tare da haifar da hayaniya.”

Sai kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani martani daga bangaren Sanata Bwacha.