An yi wa Janar-Janar kusan 100 canjin wurin aiki
Babban Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Tukur Buratai ya gudanar da wani gagarumin garambawul a rundunar sojin kasar nan, inda aka yi wa janar 94 sauyin wurin aiki. Wata sanarwa da ta fito daga kakakin sojin Najeriya Kanar Sani Kukasheka ta ce garambawul din ya shafi manyan jami’an soja 334, da suka hada da manyan […]
Babban Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Tukur Buratai ya gudanar da wani gagarumin garambawul a rundunar sojin kasar nan, inda aka yi wa janar 94 sauyin wurin aiki.
Wata sanarwa da ta fito daga kakakin sojin Najeriya Kanar Sani Kukasheka ta ce garambawul din ya shafi manyan jami’an soja 334, da suka hada da manyan jami’an hedkwatar soja da na hedkwatar tsaro da manyan rundunonin soja da kwamadoji.
Manyan hafsoshin da garambawul din ya shafa sun hada da masu mukamin Manjo Janar 37 da Birgediya Janar 57, sai Kanar-Kanar 128 da Laftana Kanar da dama da sauransu.
Daga cikin wadanda garambawul din ya shafa akwai kwamandojin runuduna ta daya da ta biyu da ta uku da ta 81 da ta 82 da kwamandojin tabbatar da tsaro da ke Neja-Delta da Jos.
Jami’an da lamarin ya shafa sun hada da Manjo Janar MA Koleoso sabon Kwamandan TRADOC da Manjo Janara SN Mu’azu da ya koma hedkwatar sojin kasa daga runduna ta biyu sai Manjo Janar MT Ibrahim da ya zama Kwamandan Kwalejin NDA, Kaduna, sai Manjo Janar LKJ Ogunewe Babban Jami’in Tsare-Tsare na Soja sai Manjo Janar FO Alli, Babban Jami’n Horarwa da Ayyuka sai Manjo Janar AA Salihu, Babban Jami’in Samar da Kayayyaki.
Manjo Janar AG Okunola Kwamandan JTF a yankin Neja-Delta, sai Manjo Janar TC Ude, Kwamandan STF a Jos. Manjo Janar LW Wiwa, Na’ibin Kwamandan Cibiyar Tsugunar da Soja, sai Manjo Janar A Oyebade Kwamandan Runduna ta daya, Manjo Janar LC Ilo, Kwamandan Runduna ta Biyu; Manjo Janar H Umaru, Kwamndan Runduna ta Uku; Manjo Janar IH Edet, Kwamandan Runduna ta 81, sai Birgediya Janar Ibrahim Attahiru Mukaddashin Kwamandan Runduna ta 82, yayin da Kanar R Abubakar Mukaddashin Daraktan Labarai na Hedkwatar Tsaro da sauransu.