An yi wa kananan yara 55 fyade cikin watanni 3 a Zariya

A watan Mayu an kawo mana yara 28 da aka yi wa fyade.

An yi wa kananan yara 55 fyade cikin watanni 3 a Zariya

Fydae

Rahotanni sun bayyana cewa an yi wa akalla kananan yara 55 fyade cikin watanni uku bana a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Shugabar cibiyar da ke kula da wadanda aka ci zarafinsu musamman kananan yara ta hanyar fyade da ke Asibitin Kofar Gayan a Zariya, Hajiya Aisha Ahmed ce ta bayyana hakan da cewa a tsakanin watan Maris zuwa Mayu an kawo masu yara 55 da aka yi wa fyade.

Hajiya Aisha ta bayyana haka ne a lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga Babban Jami’in ‘Yan Sanda mai kula da shiyyar Zariya, ACP Ahmed Lawal a ofishinsa da ke Sabon garin Zariya.

Hajiya Aisha Ahmed ta ce “a tsakanin watan Maris zuwa Mayun wannan shekara aka sami wadannan matsalolin a yankin Zariya.”

Ta yi bayanin cewa a watan Maris kadai, sun sami wadannan matsaloli har sau 16, a watan Afrilu kuma sau 11 sai kuma a watan Mayu inda suka karbi wadannan matsaloli har sau 28.

Da take nata jawabin, Shugabar Kungiyar Lauyoyi Mata shiyyar Zariya, Dokta Lateefat Bello, ta bukaci a sami wani majalisi tsakanin ’yan sanda da lauyoyi da kuma cibiyar kula da wadanda aka ci zarafin su don magance matsalar tare da fadakar da al’umma illar bata rayuwar kananan yara.

Ta bayyana cewa “babu shakka yin fyade ga kananan yara sai karuwa yake yi ba kaukkautawa wanda hakan ba karamin ci baya ba ne ga al’umma musamman a wannan karni na wayewa.”

Da yake nasa jawabin, ACP Lawal Bello ya ce a duk rana sai sun sami rahoton matsalolin fyade wadda aka yi wa kananan yara a yankunan da ’yan sandan shi ke gudanar da ayyukan su.

ACP Bello ya bayyana goyon baya da hadin kan rundunar ’yan sanda wajen kokarin zakulo masu irin wannan mummunan hali domin hukunta su.