An yi wa kifi tiyatar da ta ci N168,000 a bakinsa
Bayan tiyatar ya samu lafiya fiye da yadda ya kasance a watanni baya.
Mafi yawan jama’a a duk abin da suka samu nasara sukan dauki darasin rayuwa da mutuwa.
Amma wata mai suna Bluebell mai shekara 17 tana matukar son kifin da take kiwo inda ta iya fitar da kudin da ya kai fam 300 (kimanin Naira dubu 168 da 400) don yi wa kifinta tiyata a baki.
- Ra’ayi: Wai shin ciyo bashi halal ne ga dukkan gwamnati?
- Ranar Talata za a bude layukan sadarwa a Zamfara – Gwamna Matawalle
Likitar dabbobi Bet Hannah Jessup ta ce, Bluebell tana amfani da hannu wajen ciyar da kifin kuma tana shafa bayan kifin.
Amma bayan wani lokaci, “Mamallakiyar kifin ta lura da tarin wani abu da yake tsirowa a bakin kifin, wanda ya fara yi wa kifin illa don haka muka ga ya dace mu raba kifin da matsalar,” inji ta.
Ta ce, “Don haka sai muka yi wa Bluebell rajista domin a yi wa kifinta tiyata a cire dunkulen da ke bakin kifin. Wannan shi ne karo na biyu da aka sanya ni a cikin masu yi wa kifi tiyata, amma wannan shi ne karo na farko da na jagoranci aikin tiyatar.
“Bayan yi wa kifin tiyata ya yi barci, a lokacin da ya farfado ya fara nuna alamun samun lafiya, inda dauki awa daya a kwance.”
An dauki kifin da sauri an mayar da shi cikin ruwan da yake rayuwa. Bayan tiyatar ya samu lafiya fiye da yadda ya kasance a watanni baya.
Hannah ta ce: “Shiryeshiryen tiyatar sun fi rikitarwa, saboda yin amfani da maganin da zai sa shi barci, yayin da bayan barcin ya farka a wani yanayi. Mun kuma ba kifin maganin kashe jin zafi bayan da aka yi masa tiyatar.
“Mun yi nazari da bin diddigi a kan lafiyar kifin don binciko duk wata matsala, kuma mun gano yana da cikakkiyar lafiya kuma yana cin abinci fiye da yadda yake yi a watannin baya