An yi wa malamin makaranta sauyin wurin aiki ta hanyar canki-canki
Hukumomin ilimi na kasar Saudiyya na binciken yadda aka yi wa wani malamin makaranta sauyin wurin aiki, ta hanyar jefa kwandala aka ce ya canki Sarki ko damara?” Malamin mai suna Fahd Al Daghmani da ke koyarwa a makarantar elemantare ta garin Tarif da ke Arewacin Saudiyya, ya ce shugaban makarantar da yake aiki, ya […]
Hukumomin ilimi na kasar Saudiyya na binciken yadda aka yi wa wani malamin makaranta sauyin wurin aiki, ta hanyar jefa kwandala aka ce ya canki Sarki ko damara?”
Malamin mai suna Fahd Al Daghmani da ke koyarwa a makarantar elemantare ta garin Tarif da ke Arewacin Saudiyya, ya ce shugaban makarantar da yake aiki, ya jefa kwandala sama, inda ya ambaci sunayen wadanda yake so a sauya wa wurin aiki zuwa wata sabuwar makaranta da aka gina. Malamin ya ce ya shafe shekara bakwai yana koyarwa a makarantar, kuma babu wata hujja da za ta sanya shugaban makaranta ya dauki wannan mataki a kansa.
“Hankalina ya tashi kan matakin da shugaban makarantar ya dauka wajen jefa kwandala don canki-canki kan wanda za a sauya wa wurin aiki zuwa sabuwar makarantar,” inji Al Daghmani.
“Wannan rashin adalci ne da bai da madogara da wata ka’ida ko tsari na ma’aikatar ilimi. Ba mu taba ganin an yi amfani da canki-canki don yanke shawarar kan makomar malami ba. Mun san malamin da ya zo daga baya ne ake canja masa wurin aiki. Na shafe shekara bakwai a nan, fiye da kowane malami a fannin da na kware,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Al Shark a makon jiya.
Babban Darakta a Ma’aikatar Ilimi na Gundumar, ya sanya a gudanar da bincike, kuma ya bukaci shugaban makaranta ya bayyana dalilinsa na sauya wa Al Daghmani wurin aiki da hanyyar da aka bi wajen yin haka.
Malamin ya ce ya koma sabuwar makarantar, amma ya mika takarda ga shugaban makarantarsa ta da, da hukumomin ilimi, inda ya soki lamirin sauya masa wurin aiki, ya kuma bukaci a dawo da shi tsohuwar makarantarsa.