An yi wa manyan sojoji 7 ’yan asalin Jihar Kebbi ƙarin girma

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Nijeriya da ke sahun gaba a yawan jami’an soji manya da kanana.

An yi wa manyan sojoji 7 ’yan asalin Jihar Kebbi ƙarin girma

Nasiru Idris

Rahotanni sun bayyana cewa an ɗaga likafar wasu manyan sojoji bakwai ’yan asalin Jihar Kebbi zuwa mukamin janar-janar a rundunar sojin Najeriya.

Da wannan ne gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dokta Nasir Idris take taya sojojin murna dangane da samun karin girma.

Bayanai kamar yadda rundunonin sojin kasar suka sanar, karin girman ya haɗa da sojin kasa na sama da kuma na ruwa.

A cewar Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kebbi, Alhaji Yakubu Ahmed BK, Gwamna Nasir ya bayyana farin cikinsa dangane da karin girman da aka yi sojojin bakwai ’yan asalin jiharsa.

Daga cikin sojojin da aka ɗaga likafar tasu a bangaren sojin kasa akwai Manjo-Janar WB Idris da Manjo-Janar M Adamu daga Karamar Hukumar Ngaski, sai Manjo-Janar GS Mohammed na Karamar Hukumar Bagudu da kuma Manjo-Janar GA Suru daga Karamar Hukumar Suru.

A bangaren sojin ruwa da na sama kuma, akwai Commodore SM Tasi’u daga Karamar Hukumar Yauri da Air Vice Marshal ZA Usman a Karamar Hukumar Birnin Kebbi da kuma Air Commodore SM Chindo na Karamar Hukumar Argungu.

Alhaji Yakubu ya bayyana cewa gwamnati da al’ummar Jihar Kebbi sun yi farin ciki da wannan mataki da ya bayyana a matsayin ci gaba.

Kwamishinan ya kuma ce gwamnatin Kebbi tana alfahari da sojojin da aka yi wa karin girman musamman yadda suka yi tsaye wajen ganin an shawo kan matsalar tsaron da ke addabar Nijeriya.

“Muna godiya da kuma alfahari da wadannan sojoji masu kishin kasa da suka yi tsayin daka a fannin aikin soji da ya ba su damar kai wa inda ake bukata.

“Akwai bukatar mutane su ci gaba da gudanar da addu’o’i ga jami’an tsaron domin ganin an kawar da ’yan bindiga da sauran bata garin da suka addabi al’ummar Nijeriya.

Kazalika, gwamnan ya yi kira ga manyan sojojin da su kara kaimi don tabbatar da kiyaye doka da oda a Nijeriya.

Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Nijeriya da ke sahun gaba a yawan jami’an soji manya da kanana a yankin Arewa maso Yamma.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji