An yi wa mara lafiya dashen ƙodar alade a Amurka
Shi ne karon farko da aka samu nasarar yi wani marar lafiya dashen kodar da ke gargarar karshe.
Likitoci sun yi wa wani mutum dashen ƙodar alade a babban Asibitin birnin Boston na Jihar Masschusetts da ke Amurka.
Wannan dai shi ne karon farko da aka samu nasarar yi wani marar lafiya dashen ƙodar alade da ya sha fama da jinyar ciwon ƙoda da ke gargarar karshe.
- ‘Ana bai wa waɗanda ba su cancanta ba kwangiloli na miliyoyin Naira a Kano’
- ‘Yan bindiga sun sace fasinjoji a hanyar Katsina
Kafofin watsa labarai sun ruwaito cew likitocin sun shafe tsawon sa’o’i 4 suna tiyatar dasa ƙodar bayan an jirkita kwayoyin halittarta.
Bayanai sun ce an yi dashen kodar ne ga marar lafiyar mai suna Richard Slayman mai shekaru 62, wanda ya jima yana fama da hawan jini da ciwon suga wato diabetes.
Sai dai kuma wannan ba shi ne farau ba, domin kuwa an taba yi masa dashen ƙodar a shekarar 2018, amma bayan shekaru biyar ta lalace har aka fara yi masa wankin ƙoda.
Babban asibitin dai ya ce masu fama da ciwon ƙoda sama da dubu daya da dari hudu ne ke jiran aikin dasa musu wata kodar bayan lalacewar ta su.
A baya can an taba yin aikin sanya ƙodar aladen ga wani mutum da kwakwalwarsa ta mutu, amma na yanzu shi ne aikin farko ga wanda yake raye.
Haka zalika an taba dasa wa wasu mutane biyu zuciyoyin aladen, amma daga bisani suka mutu kasa da watanni biyu da aikin.