An yi wa marayu 120 gata a Masarautar Mutum Biyu

kungiyar Cigaban Masarautar Mutum Biyu da ke karamar hukumar Gassol, Jihar Taraba ta dauki nauyin karatun marayu 120 daga aji daya na makarantar Firamare har zuwa aji shidda.  Marayun sun hada da yara maza da mata wadanda aka dauko daga sassan masarautar kuma har ma sun fara karatu a makarantu guda biyu wadanda ke garin […]

An yi wa marayu 120 gata a Masarautar Mutum Biyu

kungiyar Cigaban Masarautar Mutum Biyu da ke karamar hukumar Gassol, Jihar Taraba ta dauki nauyin karatun marayu 120 daga aji daya na makarantar Firamare har zuwa aji shidda.

 Marayun sun hada da yara maza da mata wadanda aka dauko daga sassan masarautar kuma har ma sun fara karatu a makarantu guda biyu wadanda ke garin Mutum biyu.

A cikin wani bikin kaddamar da wannan shiri wanda ya samu halartar jama’a masu yawa a fadar sarkin Mutum Biyu, jama’a sun nuna gamsuwa da farin ciki kan wannan namijin kokari da kungiyar ta yi na  taimaka wa marayu su samu ilimin zamani.

A cikin jawabinsa shugaban kungiyar, Alhaji Tukura Julde ya bayyana cewa manufufin kungiyar ita ce bunkasa ci gaban masarautar ta fuskoki daban daban tare da bunkasa matsayin ilimin addini da na zamani.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa an bar al’ummar Hausawa da Fulani a baya ta fuskar ilimin zamani, amma a masarautar ta Mutum Biyu yanzu, kowa ya rungumi ilimin zamani wanda ya sa yara maza da mata ke zuwa makaranta kamar yadda ya kamata.

Ya ce ganin haka ne kungiyar ta ga ya kamata a taimaka wa marayu su samu ilimin zamani kamar yadda masu iyaye ke samun damar zuwa makaranta.

Ya ce sai gashi wani mai kishin masarautar ya taimaka da kudade masu yawan gaske dun gudanar ta shirin na tura yara marayu makaranta. Kuma cikin marayun  akwai musulmai kiristoci har ma da ‘yan kabilar Igbo guda uku.

Alhaji Muktari Bala wanda ya yi magana a madadin wadanda ke lura da marayu ya bayyana cewa wannan karamci da kungiyar ta nuna ya share wa marayu hawaye, domin a cewarsa akwai hazikai masu yawa daga cikin marayun amma sabo da rashin wandanda za su daukin nauyi karatunsu.

Ya kara da cewa da yawa daga cikin maruyun da suka samu shiga makaranta suna murna domin ganin cewa suma za su samu ilimi kamar wadanda iyayensu ke raye. Ya yi fatar Allah Ya saka wa dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin an taimakawa marayu ta hanyoyi daban daban. 

A cikin jawabinsa sarkin Mutum- Biyu, Alhaji Sani Kachalla ya nuna gamsuwarsa da kokarin kungiyar na kawo ayyukan ci gaba da zaman lafiya a masarautar. Ya ce kungiyar tun kafa a shekara 1976 ta taimaka wajen bunkasa matsayin ilimi da aikin gona da kasuwanci wanda yasa  aka sami ci gaba ta fuskan ilimin zamani da zamantakewar al’umma.

Alhaji Sani Kachalla ya bayyana cewa matsalar zaman banza da yawan aikata laifuka a tsakanin matasa na faruwa ne sabo da rashin ilimi mai inganci.

Alhaji Sani Kachalla ya kuma jawo hankalin yara da suka ci moriyan wannan shiri da su maida hankalinsu wajen karatu domin akwai wasu marayun masu yawan gaske wadanda basu samu damar shiga wannan shiri ba.

Ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da ke yankin da su taimaka wajen fadada wannan shiri domin wasu marayun su ci gajiyar shirin.  

 Shugaban ‘yan kabilar Igbo da ke zaune a masarautar, Mista  Kenet Ugoeze ya nuna godiya  ga kungiyar bisa daukan nauyin karatun marayu ‘yan kabilan Igbo su uku .

Ya ce wannan ya nuna irin kauna da nuna halin zaman takewa mai kyau da kungiyar ke nunawa ga sauran kabilu da mabiya addinai daban daban a masarautar. Sannan ya ce  wannan karamci zai taimaka wajen hada kan ‘yan Najeriya.

Mista Kenet Ugoeze ya ce ‘yan kabilar Igbo na zaune a masarautar Mutum Biyu ba tare da wata  tsamgwama ba, sannan ya ce ya kamata ‘yan uwansa ‘yan Igbo da ke can yankin Kudu maso Gabas su rungumi Hausawa da sauran kabilu da suke zaune a can su zauna dasu lafiya.

Wakilinmu ya ziyarci makarantu biyu inda  aka  kai yaran marayu a garin na Mutum Biyu wato makarantar Al’imam da Best Center. A makarantar Al’imam akwai marayu 100 a makarantar Best center kuma akwai Yara 20 kuma dukkansu sun fara karatu.

 

Shugabannin makarantun  biyu sun shaida wa wakilinmu cewa kungiyar ta biya kudade masu yawan gaske domin karatun  marayu wanda zai kai na tsawon shekaru shida.