An yi wa marayu 200 kaciya a Fika

A ranar Alhamis din makon jiya ne, Sarkin Askar Potiskum a Masarautar Fika ta Jihar Yobe, Dokta Aminu Abdullahi, ya gudanar  da taron yi wa yara marayu kaciya kyauta; a wani abu da ya kira ‘koyi da halayen kirki na Sarkin Fika’. Dokta Aminu Abdullahi, ya ce zama da Mai martaba Sarkin Fika da yake […]

An yi wa marayu 200 kaciya a Fika

Wadansu daga cikin yaran da aka yi wa kaciya a Potiskum

A ranar Alhamis din makon jiya ne, Sarkin Askar Potiskum a Masarautar Fika ta Jihar Yobe, Dokta Aminu Abdullahi, ya gudanar  da taron yi wa yara marayu kaciya kyauta; a wani abu da ya kira ‘koyi da halayen kirki na Sarkin Fika’.

Dokta Aminu Abdullahi, ya ce zama da Mai martaba Sarkin Fika da yake yi ne ya sa ya koyi wasu dabi’unsa na tausaya wa marayun da aka kashe iyayensu a hare-haren Boko Haram, wanda hakan ya sa shi ma ya koyi irin wannan hali ya gayyaci sarakunan Aska na Arewa don yin kaciya kyauta ga marayu a garin Potiskum.

Ya ce a lokacin baya idan ya fita yin kaciya ta kudi yana cin karo da wadansu mata su kawo maraya su ce ba su da kudi amma ga Naira 500 ko 700 a yi masa kaciya; shi kuma sai ya yi wa yaron ya ce ta bar kudin ta saya masa abinci. Ganin hakan na yawa ne ya ware rana guda ya dauki nauyin yi wa marayu 100 kaciya, kuma kafin a gama sai da aka yi wa yara marayu sama da 200.

“Ni na tanadi kudina ban ce kowa ya ba ni gudunmawa ba. Na gayyaci Kungiyar Wanzamai ta zo mu yi wannan kaciya fisabilillahi a kofar gidana; jin haka ne ya sa Sarkin Fika ya ce in zo kofar fada a yi wannan taro kuma ya bada tasa gudunmawar ta duk abincin da za a ci a wajen,” inji Sarkin Askar.

Ya ce kafin gudanar da kaciyar ya buga fom-fom ya sa aka raba kyauta a dukkan zawiyyoyi da masallatai da majalisu ta hannun dagatai da jaurabai domin su suka fi sanin inda marayun suke. Ya ce ta haka ne aka zakulo marayun: “Yara 100 na yi niyya, amma sai ga yara 178, kafin mu gama kaciyar inda aka yanke yara sama da 200 domin duk wanda ya zo wucewa ya ga mutane idan ya tambaya aka ce masa kaciya ake yi – sai ya bada yaronsa a yi masa idan biyan za a yi Naira 2,000 ake yi wa kowane yaro,” inji shi.

Mai martaba Sarkin Fika Alhaji Muhammadu Ibn Abali Muhammadu Idrissa, ya yaba wa wanzaman bisa yadda suka rike sana’arsu ta gado ba su bar ta ta bace ba.

Ya kuma jinjina wa Kungiyar Wanzaman kan yadda ta yi wa Sarkin Askar Potiskum Dokta Aminu Abdullahi kara ta hanyar zuwa su taya shi wannan hidima wanda hakan ya kara nuna wa duniya kan wanzamai a hade yake kuma Masarautar Fika na tare da Sarkin Askar Potiskum.

Ya ce a tarihi ba su taba ganin inda aka tara jama’a haka don yi wa marayu kaciya kyauta ba sai yanzu inda ya ce shi ne karon farko a iya saninsa.

Da yake godiya a madadin Sarakunan Aska, Sarkin Askar Gombe Sani Sambo, ya shaida wa Mai martabar cewa su wanzamai sun zo ne don karfafa sana’arsu ta gado domin wanzamai da masarauta suke tinkaho, kuma a Potiskum Sarkin Fika, yana ba su dukkan goyon bayan da suke bukata.

Alhaji Sani, ya kara da cewa Sarakunan Askar Arewa kaf sun halarci wannan taro kama daga kan shugabansu Sarkin Askar Kano Dokta Yunusa Nabango da Sarkin Askar Ibbi da na Argungu da na Misau da sauransu duk suna wajen.

Shugaban Majalisar Sarakunan Askar Najeriya Sarkin Askar Kano Muhammad Yunusa Nabango, ya ce wannan taro ya kayatar domin shi ne irinsa na farko da suka taba yi don yi wa marayu kaciya kyauta, amma taron kaciya wa yara da ba marayu ba sun yi sau biyar.

Dokta Nabango, ya jinjina wa wanzaman bisa amsa gayyatar Sarkin Askar Potiskum inda ya yi kira ga sauran da su yi koyi da shi.

Alhaji Muhammad Yunusa Nabango da taimakon Sarkin Fika Alhaji Muhammadu Ibn Abali Muhammadu Idrissa, ya kaddamar da kaciyar a kofar fadar Sarkin Fika da ke garin Potiskum.