An Yi Wa Mata Masu Yoyon Fitsari 28 Aiki Kyauta a Sakkwato

Likitoci sun bayyana cewa yin aikin tiyata na warkar da larurar gaba daya

An Yi Wa Mata Masu Yoyon Fitsari 28 Aiki Kyauta a Sakkwato

Wasu mata da ke fama da larurar yoyon fitsari a Jihar Sakkwato sun bayyana farin cikinsu kan aiki kyauta da Gidauniyar Yaki da Yoyon Fitsari ta Najeriya (FFN) ta dauki nauyin yi musu.

Matan da suka amfana sun yi kira ga sauran masu larurar da su ma su zo su ci gajiyar wannan aikin kyauta, kasancewar ana warkewa sarai idan aka yi.

Larurar na daga cikin matsalolin da doguwar nakuda ke haifarwa, idan ba a samu kulawar likitocin da suka dace ba.

Sai dai kamar yadda likitoci ke bayyanawa, yin aikin tiyata na warkar da larurar gaba daya.

Kungiyar ta FFN da hadin guiwar Asusun Bayar da Tallafi na Majalisar Dinkin Duniya ne suka yi wa mata 28 masu larurar yoyon fitsari aikin kyauta a Sakkwato, daga ranar 23 zuwa 27 ga watan Mayu, 2022.

Matan da suka ci gajiyar aikin dai na Asibitin Mata da Yara na Maryam Abacha da ke Sakkwao, suna ci gaba da samun kulawa.

Daraktan kungiyar, Musa Isa, ya ce daukar nauyin yi wa matan aikin na daga cikin ayyukansu na wayar da kai kan cutar yoyon fitsari na 2022.

Taken bikin na bana dai shi ne “Kawo karshen cutar Yoyon Fitsari: Zuba jari a bangaren kiwon lafiya mai inganci, shi ne babban jarin al’umma”.

Abin da wata mai larurar ke Cewa

Wata matar aure mai shekara 15, Azima Isiya, da ke kauyen Dankurmi a Karamar Hukumar Gumi ta ce satinta biyu tana dakon layi ya zo kanta a yi mata aikin kyauta.

Ta kuma ce an mata aure ne lokacin da take da shekara13, kuma ta gamu da larurar ne bayan haihuwarta ta farko a Asibitin Bena da ke Karamar Hukumar Zuru da ke Jihar Kebbi.