An yi wa matashin da ya mayar da tsintuwar N15m tayin auren mata 4

Ƙungiyar Masu Dalilin Aure sun yi tayin auren mata hudu ga matashin mai baburin A-Daidata-Sahun nan da ya tsinci Naira miliyan 15 ya mayar wa mai su

An yi wa matashin da ya mayar da tsintuwar N15m tayin auren mata 4

Ƙungiyar Masu Dalilin Aure (Mai Dalili) a Jihar Kano sun yi wa matashin mai baburin A-Daidata-Sahun nan da ya tsinci Naira miliyan 15 ya mayar wa mai su, tayin auren mata hudu.

Auwalu Salihu mai shekaru 22 na ci gaba da samu yabo tun bayan da da ya tsinci Naira miliyan 15 na wani dan ƙasar Chadi da ya zo Kano sayayya ya nanta a babur dinsa, ya kuma mayar masa da kudin.

Kungiyoyi da jami’an gwamanti da attajirai sun yi ta yi masa kyaututtuka domin yaba wa kyakkyawan halinsa, ciki kuwa har da wani dan kasuwa da ya ba shi kyautar sabon babur mai kafa uku.

Daga cikinsu, kungiyar Mai Dalili ta yi masa alkawarin auren mata hudu da zai zaba daga cikin 10 da ta ware masa.

A hirarsa da Freedom Radio, Shugaban Kungiyar, Alhaji Mukhtar Inuwa Yakasai, ya bayyana cewa biyu daga cikin matan da kungiyar ta ware wa matashin ’ya’yansa ne.

Ya ce gaskiya da rikon amana da Auwal ya nuna ne suka sa ya cancanci wannan karrama wa.

“Matashin ya nuna kyawawan dabi’u irin na Manzon Allah (SAW), wanda tabbas amintacce ne.

“Shi ya sa muka yanke shawarar yi masa wannan karimci.

“Akwai mata 10 da zai zabi hudu daga ciki. Biyu daga cikinsu kuma ’ya’yana ne.”

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan