An yi wa mawaki aiki a kwakwalwarsa yana kaka jita
Wani mawaki a kasar Indiya, Abhishek Prasad ya kankame jitarsa a lokacin da ake yi masa tiyata a kwakwalwa, ta yadda ya taimaka wa likitoci suka fahimci inda ya dace su yi masa aikin fika. Mutumin mai shekara 37, ya yi fama da wata cuta ta kaurewar jijiyoyin nama da ke kai sako kwakwalwa (dystonia) […]
Wani mawaki a kasar Indiya, Abhishek Prasad ya kankame jitarsa a lokacin da ake yi masa tiyata a kwakwalwa, ta yadda ya taimaka wa likitoci suka fahimci inda ya dace su yi masa aikin fika. Mutumin mai shekara 37, ya yi fama da wata cuta ta kaurewar jijiyoyin nama da ke kai sako kwakwalwa (dystonia)
Don haka ya zame wa likitoci dole su yi masa aiki yana farke, ta yadda za su gano sashen kwakwalwar d ake da alaka da kaurewar naman jikinsa, musamman yatsun hannunsa na hagu. Shi ya sa ya yanke wa kansa shawarar kaka jita.
Wannan aiki da aka yi masa shi ne irinsa na takwas da aka tava yi a duniya, alhali majiyacin yana farke, kamar yadda asibitin Bengaluru’s Bhagwan Mahaveer ya bayar da sanarwa.
“An huka kofa mai zurfin milimita 14 a kansa, sannan aka tura zungurun lantarki cikin kwakwalwar bayan an kashe masa jin zafin ciwo,” a cewar sharan Srinivasan, wani kwararren likitan fikar kwakwalwa.
Prasada ya cika da mamakin sakamakon aikin da aka yi masa, domin ya dake yana fama da ciwon tun a shekarar 2015, al’amarin da ya kusa kawo karshen sana’arsa.
Ya yi ta kai-kawo a asobitoci wajen neman magani, amma mafi yawan likitoci ba su gano hakikanin abin da ke damunsa ba; kumsa ba su lura da kaurewar jijiyoyin da ke aikewa da sakonni zuwa kwakwalwa ba, kan cewa su ke haifar masa da matsalar.
“Al’amarin ya yi matukar sosa mini rai ni da iyalina. Wannan dais hi ne abin da na dake ina jira,” in ji Prasad, wanda ya yi watsi da aikinsa na fasahar sadarwa ya tsunduma cikin kake-kake da raye-raye.
“Lamarin na da matukar tayar da hankali da dugunzuma cikin damuwa. Na sha yin kuka saboda wannan matsalar. Kowace safiya nakan tashi in kaka kuntuggina. Sai dai bayan mintuna biyar sai in yi watsi da abin.” Wannan cuta dai an kiyasta a kalla kasha guda zuwa biyu cikin 100 na mawaka na fama da ita.
Bayan da aka yi masa tiyata ranar 11 ga Yulin bana, yana bukatar a kauki wasu makonni da za a yi masa aikin motsa jiki don ya wartsake, ya koma bakin aikinsa ba tare da jin zafin ciwo ba.
“Burin a na farko shi ne in fitar da kundin faya-fayan waka nan da karshen shekara ko tsakiyar shekara mai kamawa,” inji Prasad.