An yi wa mutane 500 magani kyauta a Zariya

Dalibai sun dauki nauyin wannan shirin don ganin sun saka wa al’ummar Tudun Wada da alheri.

An yi wa mutane 500 magani kyauta a Zariya

Likitoci

Kimanin mutane 500 da ke fama da cututtuka daban-daban ne suka amfana da magani kyauta a a unguwar Tudun Wada da ke Zariya.

Daliban sashen nazarin aikin jinya da ke Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ne suka shirya taron wayar da kan jama’a da rabon magani kyauta mai taken “Medics World”.

Daliban sun gudanar da wannan aiki ne a unguwar Tudun-Wada da ke Zaria, inda suka bada magunguna kala-kala ga marasa galihu da ke fama da ciwo iri-iri. .

Shugaban tawagar, Abdullahi Mohammed Sani, ya ce wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya na daga cikin ayyukan sa-kai da ya kamata a riƙa yi wa al’umma.

Ya ce, “a matsayinmu na dalibai a bangaren jinya, akwai hakkin al’umma da rataya a wuyanmu, musamman hakkin bayar da gudunmuwa a bangaren inganta kiwon lafiyarsu, don haka muka yanke shawarar sauke wannan nauyi ta bangaren bayar da tallafi. ”

Abdullahi ya ce “Dalibai ne suka dauki nauyin wannan shirin a kokarinsu na ganin sun saka wa al’ummar Tudun Wada da alheri, saboda irin kara da jama’ar suke nuna musu a matsayin masu masaukin baki gare su.”

Ya jaddada cewa gidauniyar na shirin sake irin wannan taron na wayar da kan jama’a da bada magani kyauta in Allah Ya kaimu bayan Sallah da nufin fadada ayyukan ga sauran al’umma a Zariya.

Ya bayyana bukatar ba da tallafi da hadin kai ga gidauniyar, domin samun karin nasarori.

Malama Salamatu Nagogo, wata malama a sashen koyon aikin jinya, ta ce hidimar al’umma na daga cikin horon da ake bai wa daliban a lokacin karatunsu.

Ta kuma bukaci daliban da su kara fadada aikinsu domin kara adadin mutanen da za su amfana da shirin.

Bello Azeeza, kakakin gidauniyar ta ce ayyukan da aka gudanar a shirin na rana daya sun hada da gwajin cutar sukari da kuma gwajin cutar zazzabin cizon sauro kyauta.

Azeeza ta kara da cewa, kwararru a fannoni da dama sun gudanar da jawabin kiwon lafiya kyauta kan cututtukan da ke addabar jama’a a ’yan shekarun nan.

Tahir Isiyaku, wanda ya ci moriyar tallafin ya bayyan jin dadinsa kan wannan yunkuri, yana mai cewa shirin zai yi amfani matuka gaya ga marasa lafiya da ba za su iya biyan kudin magani ba.