An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS
An yi wa mutane damafar da ta kai Naira biliyan 52 a Najeriya ta hanyar tura kuɗi ta banki

Damfarar da aka yi wa mutane ta hanyar tura kuɗi ta banki ya ninku sau uku zuwa Naira biliyan 52 a Najeriya.
Alƙaluma ‘n Hukumar Kula da Tsarin Tura Kuɗi Tsakanin Bankuna (NIBSS) ya nuna a shekara huɗu da suka gabata aka samu wannan karin daga Naira biliyan 11 zuwa biliyan 52,
Alƙaluman sun nuna a shekara shekarar 2024 an yi asarar Naira biliyan 52, kusan ninki biyar na Naira biliyan 11,2 da aka yi asara a shekarar 2020.
Rahoton na NIBSS ya bayyana cewa masu damfarar sun yi yunƙurin sace Naira biliyan 86.4 a shekarar 2024.
The figure is coming on the heels of the latest GDP figures released by the National Bureau of Statistics showing a fourth quarter 2024 growth of 3.8 percent, the fastest in three years, driven by the services sector, including finance and insurance.
“Satar da ’yan damfara suka yi wa mutane ta hanyar hadahadar kuɗi ta zamani ta ƙaru saidai a cikin shekaru biyar da suka gabata,” in ji rahoton na NIBSS.
Ya ci gaba da cewa, “’yan damfarar na amfani da dabaru iri-iri, ciki har da amfani da bayanan tsofaffi ko ƙananan yara ko ’yan ƙasashen waje ko kuma a bayanan mutane ba da saninsu ba, wajen buɗe asusun banki.
“An gano yadda aka sace Naira miliyan 400 ta hanyar amfani da asusun da aka buɗe da bayanan mutane ba da saninsu ba ko kuma tsofaffi,” in ji rahoton.
Ya bayyana cewa an yi nasarar ƙwato wasu daga cikin kuɗaɗen sannan ana b’cingabda bincikar jami’an bankin da ake zargin hannunsu a badaƙalar.