An yi wa mutane miliyan biyu gwajin HIV a Gombe

An yi wa mata masu juna biyu 13,000 gwaji, inda 235 daga cikinsu suka samu magani

An yi wa mutane miliyan biyu gwajin HIV a Gombe

Cibiyar Shirye-shiryen Lafiya (CIHP) ta sanar cewa fiye da mutum miliyan biyu ne suka amfana daga gwajin cutar HIV/AIDS da magunguna da shawarwari da sauransu a Jihar Gombe cikin shekaru 17 da suka gabata.

Shugabar cibiyar, Dokta Bolanle Oyeledun, ta bayyana hakan yayin ziyararta mataimakin gwamnan jihar, Manassah Jatau, a Gombe.

Dokta Oyeledun ta ce CIHP ta kammala shekaru 17 na shirin yaki da HIV/AIDS tare da nasarar shawo kan cutar da inganta lafiyar al’umma.

Ta kara da cewa, “CIHP ta kasance ginshiki a yakin da cutar HIV/AIDS a jihar, inda ta yi wa fiye da mutum miliyan biyu gwaji, mutum 26,000 suka samu magunguna.

“Yaɗuwar cutar ta ragu sosai, kuma Gombe tana daga cikin jihohin Najeriya uku da suka cimma nasarar shawo kanta.”

Ta jaddada cewa shirin ya gyara cibiyoyin kiwon lafiya, ya horar da ma’aikatan lafiya, da kuma yi wa mata masu juna biyu 13,000 gwaji, inda 235 daga cikinsu suka samu magani.

Ta ce, “Fiye da mata miliyan guda an yi masu gwajin HIV, kuma waɗanda aka samu suna ɗauke da cutar an ba su magani don hana yaduwarta daga uwa zuwa jariri.”

A nashi jawabi, mataimakin gwamnan, ya yaba wa shirin, yana mai cewa, “Lafiya ita ce tushen komai; ba tare da ita ba, babu wani abu da za a iya cimmawa.”

Ya ce shirin ya taimaka wajen sauya yanayin yaduwar cutar HIV da kusan kashi 97 cikin 100 a jihar.

Jatau ya bukaci kungiyoyin ci gaba su tallafa wajen gina ƙwarewa da bincike domin samar da magunguna da allurar rigakafin HIV a Najeriya.

Kwamishinan lafiya, Dokta Habu Dahiru, ya yaba wa Jami’ar Columbia, Kungiyoyin Lafiya na Duniya, da CIHP saboda ayyukan yaki da cutar HIV da nufin karfafa tsarin kiwon lafiya a jihar.

Ya kuma jaddada muhimmancin ɗorewa da tabbatar da jajircewa wajen bayar da ingantaccen kulawa ga kiwon lafiya a jihar.