An yi wa mutum 215,277 rigakafin Coronavirus a Najeriya
Mahukunta a Najeriya sun sanar da cewa an yi wa mutum fiye da 250,000 allurar rigakafin cutar Coronavirus a fadin kasar. Alkaluman da Hukumar Lafiya a matakin farko ta kasar (NPHCDA) ta fitar a ranar Talata, sun nuna cewa an yi wa mutum 215,277 allurar rigakafin a wasu jihohi 30 na kasar ciki har da […]
Mahukunta a Najeriya sun sanar da cewa an yi wa mutum fiye da 250,000 allurar rigakafin cutar Coronavirus a fadin kasar.
Alkaluman da Hukumar Lafiya a matakin farko ta kasar (NPHCDA) ta fitar a ranar Talata, sun nuna cewa an yi wa mutum 215,277 allurar rigakafin a wasu jihohi 30 na kasar ciki har da birnin Abuja.
- Uwar tagwaye ta yi wa daya zanen tattoo don bambance su
- ‘APC na bukatar mulki na shekara 32 don inganta rayuwar al’umma’
Kididdigar alkaluman sun nuna cewa an yi wa kashi 5.5 cikin dari na ’yan kasar.
A yayin da Jihar Legas ce a kan sahu na gaba da yawan mutanen da suka fi kamuwa da cutar a fadin kasar, haka kuma ita ce a kan gaba da mafi yawan mutanen da aka yi wa rigakafin da mutum 58,461.
Daga cikin jihohin da aka yi wa rigakafin akwai Adamawa (7,407), Akwa Ibom (127), Anambra (132), Bayelsa (552), Binuwe (146), Borno (653), Kuros Riba (948), Delta (915), Ebonyi (77), Edo(2,645) da Ekiti (1,049).
Sauran jihohin su ne; Enugu (956), Abuja (8,616), Gombe (203), Imo (1,908), Kaduna (14,572), Kano (3,903), Katsina (10,002), Kwara (12,016), Nassarawa (6,801), Ogun (19,257), Ondo (4,205), Osun (6,658), Filato (883), Ribas (1,951), Sakkwato (98) da Yobe (5,509).
Ragowar jihohin da ba a yi wa ko mutum daya ba a cikinsu su ne Abiya, Zamfara, Kebbi, Neja, Kogi, Taraba da Oyo.
A karshe, Hukumar NPHCDA tana shawartar mata masu juna biyu da su tuntubi likitocinsu game da fa’idar allurar rigakafin bisa la’akari da tasirinta ga lafiyarsu da kuma abin da suke dauke da shi a cikinsu.