An yi wa mutum 3 ɗaurin rai da rai kan yi wa kurma fyaɗe

Kotu ta gamsu da hujojjin da aka gabatar mata tare da yanke wa mutanen hukuncin ɗaurin rai da rai.

An yi wa mutum 3 ɗaurin rai da rai kan yi wa kurma fyaɗe

(Hoto: us.fotolia.com)

Wata Babbar Kotu da ke zamanta a Birnin Kebbi ta yanke wa wasu mutum uku hukuncin ɗaurin rai da rai sakamakon samun su da laifin yi wa wata kurma mai shekara 18 fyaɗe.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin su ne; Amiru Sani, Aliyu Umar, da Bashar Dan-Inno.

An same su da laifin haɗa baki da aikata fyaɗe a ƙauyen Wararin Zaromawa da ke ƙaramar hukumar Gwandu a jihar.

Mai gabatar da ƙara, ƙarƙashin jagorancin Faridah Muhammad, ta bayyana cewa mutanen sun kutsa gidan matar ne yayin da ta ke barci, suka ɗaure hannunta sannan suka yi mata fyaɗe.

Muhammad ta buƙaci kotu da ta zartar da hukuncin da ya wajaba kan waɗanda suka aikata laifin.

Ta bayyana cewar laifin ya saɓa da sashe na 259 da 60 na dokar manyan laifuka ta Jihar Kebbi ta 2021.

Mai kare waɗanda ake tuhuma, ya roƙi a kotun ta yi musu sassauci.

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Shamsudeen Jafar, ya bayyana cewa kotun ta gamsu da shaidun da aka gabatar mata cewar waɗanda ake tuhuma sun haɗa baki wajen aikata laifin.

Don haka alƙalin ya yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin rai da rai kamar yadda doka ta tanada.