An yi wa mutum 411 fyade a Sakkwato
Lamarin ya hada da mata da da mazan da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sanar da cewa an ci zarafin mutum 411 ta hanyar fyade cikin shekara guda a fadin Jihar.
Kwamishinar Mata da Harkokin Yara a Jihar, Hajiya Kulu Sifawa ce ta bayyana hakan yayin zantawarta da sashen Hausa na BBC.
- Harin ’Yan bindiga: Mutum takwas sun mutu a Kaduna
- ‘Mutanen Najeriya za su yaba wa Buhari a karshen mulkinsa’
Yayin taron bikin murnar zagayowar ranar yara ta bana da aka gudanar wannan mako, Hajiya Kulu ta ce lamarin ya hada da mata da aka ci zarafinsu ta hanyar lalata da kuma mazan da aka zakke musu ta dubura.
“Mun bude cibiyar da ake kira Nana Khadija, inda ake kai wadanda aka yi wa fyade domin a duba lafiyarsu, kuma muna da alkaluman matan da aka yi wa fyade da mazan da aka yi luwadi da su da aka kai kara,” inji ta.
A cewarta, a yayin da wannan lamari ke faruwa a kauyuka da birane, sun kafa wani kwamiti da ke sa ido kan wannan batu.
Ta ce yanzu haka suna jiran amincewa da sabbin kudurorin da suka gabatar wadanda za su taimaka wajen shawo kan cin zarafin mata da kare kananan yara a fadin jihar.