An yi wa Neja-Tornadoes kwaskwarima

Hukumar gudanar da kungiyar kwallon kafa ta Neja- Tornadoes ta yi wa kungiyar kwaskwarima a daya daga cikin matakan da take dauka na cika sharuddan Hukumar Kula da Harkokin kwallon kasa ta kasar nan wato Nigerian Football Federation (NFF) kasancewar ta daya daga cikin sabbin kungiyoyin da za su fafata a gasar cin kofin GLO […]

An yi wa Neja-Tornadoes kwaskwarima
An yi wa Neja-Tornadoes kwaskwarima

Hukumar gudanar da kungiyar kwallon kafa ta Neja- Tornadoes ta yi wa kungiyar kwaskwarima a daya daga cikin matakan da take dauka na cika sharuddan Hukumar Kula da Harkokin kwallon kasa ta kasar nan wato Nigerian Football Federation (NFF) kasancewar ta daya daga cikin sabbin kungiyoyin da za su fafata a gasar cin kofin GLO na bana a rukunin kwararru.

Kwaskwasrimar da aka yi sun hada da ba wasu daga cikin masu horar da ’yan wasa uku damar zuwa karo ilimi domin kara kwarewa a wannan fanni da suka mayar da hankali a kai. Sai kuma wasu 3 wadanda Hukumar ta ga sun fi dacewa su koma Ma’aikatar Kula da Harkokin Wasanni domin cigaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum yadda aka tsara musu.
Kakakin Hukumar Gudanar da kungiyar Mista George Nuhu Daniya yayin da yake yi wa wakilinmu karin haske, ya ce, ‘an daga darajar daya daga cikin Kocin da ke horar da karamar kungiyar Tornadoes wato Tornadoes Feeder Team mai suna Muhammad Bello wanda zai mayar da hankali wurin koya wa masu tsaron gida (goal keepers) dabarun tsare kwallo. Sannan kuma an dauko Mista Christopher Bernard da Muhammad Atiku don bunkasa kungiyar’.
Mista George Nuhu Daniya ya kara da cewa tuni kulob din Tornadoes ya sabunta kwantaragin Kocin da kungiyar ta samu nasarar fafatawa har ta kai ga shiga rukunin kwararru a gasar bana mai suna Abdullahi Usman Biffo. Ya yi watsi da jita-jitar da aka yi ta yayata wa cewar kungiyar ta sallami wasu daga cikin masu horar da ’yan wasan da cewa babu kashin gaskiya a ciki.

Fiye da ƙungiyoyi 60 sun yi zanga-zanga kan taron G7 a Faransa

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina