An yi wa sansanonin ’yan ta’adda luguden wuta a Zamfara

Sansanonin da aka yi wa luguden wuta na fitattun ’yan ta’adda ne — Abdullahi Nasanda a Zurmi, da Malam Tukur a Gusau.

An yi wa sansanonin ’yan ta’adda luguden wuta a Zamfara

Rundunar sojojin sama ta Nijeriya ta ce jiragen yaƙinta sun yi luguden wuta a sansanoni uku na ’yan ta’adda a Jihar Zamfara.

Rundunar sojin ta ce luguden wutar ya kashe da dama daga cikin ’yan ta’addan tare da lalata maɓoyarsu a ranar Laraba.

Kakakin rundunar sojojin saman ta Nijeriya, AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis.

AVM Gabkwet ya bayyana cewa dakarunsu na rundunar Operation Hadarin Daji ne suka aiwatar da wannan gagarumin aiki.

Gabkwet ya ƙara da cewa sansanonin da aka yi wa luguden wuta na fitattun ’yan ta’adda ne — Abdullahi Nasanda a Zurmi, da Malam Tukur a Gusau, da kuma wani sansani a Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojojin saman ya ce jami’ansu sun yi amfani da na’urori na leƙen asiri a sansanin ’yan ta’adda na Nasanda inda aka hango ’yan ta’adda suna kai-komo kuma sun ɓoye baburansu.

“Bayan an tabbatar da ayyukan da suke yi irin na ’yan ta’adda, sai jirage suka yi luguden wuta a sansanonin inda suka kashe ’yan ta’adda da dama.

“Kazalika an gudanar da irin wannan leƙen asiri a sansanin Malam Tukur inda aka ga ’yan ta’adda suna kazar-kazar.

“Daga nan aka kai musu hari inda aka kashe da yawa daga cikinsu sannan aka lalata sansaninin,” in ji sanarwar.

“Haka kuma an kai hare-hare ta sama a garin Kanikawa da ke Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Zamfara, inda aka kashe ’yan ta’adda tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu,” a cewar Gabkwet.