An yi wa tawagar Aminu Ringim ruwan duwatsu a wurin daurin aure
Wasu matasa sun yi ruwan duwatsu ga ayarin dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Alhaji Aminu Ibrahim Ringim a kauyen Madaci da ke karamar Hukumar Guri da ke jihar.Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar da ta gabata lokacin da tsohon dan takarar ya wakilci tsohon Gwamnan […]
Wasu matasa sun yi ruwan duwatsu ga ayarin dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata Alhaji Aminu Ibrahim Ringim a kauyen Madaci da ke karamar Hukumar Guri da ke jihar.
Lamarin wanda ya faru a ranar Asabar da ta gabata lokacin da tsohon dan takarar ya wakilci tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido a wajen daurin auren mai daukar hoton tsohon Gwamnan, inda matasan suka farfasa wasu motocin ayarin.
Rahotanni sun ce wani direban gidan gwamnati da ya je wurin daurin auren da lamarin ya rutsa da shi, matasan sun fasa masa mota. Direban wanda ya bukaci a sakaya sunansa da ya ce shi ma an fasa masa mota ya ce an raka tawagar Aminu Ringim har wajen gari ana yi masa ihu ba ma yi.
Aminiya ta samu labarin cewa mahaifin amaryar ya rika kuka saboda bakin ciki kan yadda aka raka tawagar Aminu Ringim da jifa lokacin da suka je daurin auren ’yarsa a kauyen Madacin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa DSP Audu Jinjiri ya ce ba su samu labarin faruwar lamarin ba.