An yi wa tsofaffi uku rotse bisa zargin yi wa ’yar shekara 10 fade a Abuja

Al’ummar Unguwar Fulani da ke garin Dakwa a Abuja, sun yi wa wasu tsofaffi uku mazauna garin duka da jifarsu, sannan suka rusa dakin baca mallakar daya daga cikinsu bayan an kama su a ciki suna yi wa wata ’yarinya mai shekara 10 fyade. Mutanen uku, Garba Hussaini mai shekara 67, da Nuhu Umar mai […]

An yi wa tsofaffi uku rotse bisa zargin yi wa ’yar shekara 10 fade a Abuja

Mutanen uku da a ke zargi da yi wa yarinyar fyadeAl’ummar Unguwar Fulani da ke garin Dakwa a Abuja, sun yi wa wasu tsofaffi uku mazauna garin duka da jifarsu, sannan suka rusa dakin baca mallakar daya daga cikinsu bayan an kama su a ciki suna yi wa wata ’yarinya mai shekara 10 fyade.
Mutanen uku, Garba Hussaini mai shekara 67, da Nuhu Umar mai shekara 68 mai sana’ar fawa da Sa’idu Adamu mai shekara 75 mai sana’ar tara yashi, ana zarginsu ne da yi wa ’yarinyar fyade a ranar Juma’ar da ta gabata bayan daya daga cikinsu mai suna Sa’idu wanda shi ne ke da bacar ya aike ta ta sayo masa zobo ta kai masa dakin.
Mahaifiyar yarinyar mai suna Ramatu ta shaida wa Aminiya cewa ’yarta wadda aka sakaya sunanta na dawowa ne daga masallacin Juma’a a lokacin da wadanda ake zargin suka gamu da ita, kuma wasu mata ne da ke wani gida kusa da bacar suka ankarar da ita bayan sun gano abin da ke faruwa a dakin. Ta ce zuwanta wurin ke da wuya sai yarinyar ta fito daga dakin ba a jima ba kuma sai Sa’idu ya fito tare da mutanen biyu.
“Yana kokarin rufe wurin ne sai muka auka musu tare da jama’ar unguwa, daga bisani aka kai maganar gaban ofishin ’yan sanda na Dakwa,” inji ta.
Wani makwacin matar mai suna Surajo Kamba da ya taimaka wajen kai maganar gaban hukuma, ya ce ofishin ya umarce su kai yarinyar zuwa Asibitin Deide inda binciken likitoci ya tabbatar sun yi wa yarinyar fyade.
Ya ce an kai lamarin babban ofishin ’yan sanda na Zuba inda ake tsare da mutanen tun ranar Asabar ta makon jiya.
Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba, CSP Femi Adelagan wanda ya tabbatar da faruwan lamarin ya ce sun kammala bincikensu a kuma suna shirin mika wadanda ake zargin ga sashin CID na rundunar ’yan sandan Abuja a shekaranjiya Laraba don hukunci na gaba.