An yi wa tsohon shugaban karamar hukuma kisan gilla a Katsina

A ranar Alhamis din makon jiya ce mazauna Rukunin Gidaje na Barhim suka wayi gari an yi wa tsohon shugaban karamar Hukumar Ingawa Alhaji Sama’ila Magaji kisan gilla. Marigayin wanda wasu da ba a gano su wane ne ba suka yi wa kisan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin Sallar Isha’i bayan ya dawo […]

An yi wa tsohon shugaban karamar hukuma kisan gilla a Katsina

MD Abubakar Shugaban ‘yan sandan NajeriyaA ranar Alhamis din makon jiya ce mazauna Rukunin Gidaje na Barhim suka wayi gari an yi wa tsohon shugaban karamar Hukumar Ingawa Alhaji Sama’ila Magaji kisan gilla.
Marigayin wanda wasu da ba a gano su wane ne ba suka yi wa kisan ya gamu da ajalinsa ne a lokacin Sallar Isha’i bayan ya dawo daga Kano, kamar yadda mazauna yankin suka ce.
Ana zaton ’yan ina da kisa ne suka yi aika-aikar da ake zargin sun biyo shi ne watakila daga Kano ko sun tarbe shi a hanya inda sai a wannan wuri ne suka aiwatar da wannan mugun aiki.
Majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, wadanda suka yi kisan ba su dauki komai daga wurin marigayin ba.
Alhaji Sama’ila Magaji mai shekara sama da 60 kafin mutuwarsa shi ne zababben Shugaban karamar Hukumar Ingawa na karshe wanda har yanzu ba a sake zabe ba sai masu riko.
Kamar yadda bayanai suka nuna, kafin mutuwarsa tsohon shugaban yana harkar kasuwancin man fetur a Jihar Kano tun daga lokacin da wa’adin mulkinsa ya kare.
Wata majiya ta ce a lokacin da marigayin ya fahimci akwai wani abin da zai faru a kansa, ya yi kokarin kiran dan uwansa da suke uba daya mai suna Salisu ta waya, amma kafin Salisu ya iso wurin makasan sun ci karfin dan uwan nasa inda nan take ya garzaya ya shaida wa ’yan sanda domin kawo dauki kuma kafin iso maharan sun aiwatar da aikinsu suna shirin tafiya, amma sun yi nasarar kama daya daga cikinsu. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina DSP Aminu Abubukar Sadik wanda ya tabbatar da faruwar haka, ya shaida wa manema labarai cewa, rundunar ta kama wani matashi mai suna Abba Lawal dan garin Daura da take tuhuma tare da sauran mutum biyu da take nema a kan aikata wannan mugun aiki.
Ya ce sun samu wuka da wayoyin salula biyu da ake zargi na wadanda suka yi kisan ne.
Wata majiya ta kusa da mamacin ta ce wanda aka kama yana da dangantaka da tsohuwar matar Alhaji Sama’ila.