An yi wa tsohuwa mai shekara 80 fyade a Ondo

An tsinci gawar tsohuwar ce a gonarta bayan an kashe ta

An yi wa tsohuwa mai shekara 80 fyade a Ondo

Wasu bata-gari a garin Ore da ke Karamar Hukumar Odigbo ta Jihar Ondo, sun kashe wata tsohuwa mai suna Felicia Aderibigbe, bayan sun yi mata fyade.

Aminiya ta gano cewa an kashe tsohuwar ce a gonarta da ke kusa da garin Ore na Jihar.

Rahotanni sun nuna cewa tsohuwar, wacce ta fita daga gidanta zuwa gonar domin yin aiki, amma aka neme ta aka rasa tsawon kwanaki, kafin daga bisani wasu masu sintiri su gano gawar a kusa da gonarta.

Daya daga cikin makwabtan matar wanda yake cikin masu sintirin, Adekunle Ishola, ya ce wadanda ake zargin sun yi wa matar fyade har ta mutu, kamar yadda gawar tata ta nuna.

Ya ce a ’yan kwanakin nan, an sha samun batutuwan labaran aikata fyade a yankinsu, inda aka rika kai wa jami’an tsaro rahotannin aikata hakan.

“Wannan abin takaici ne daga cikin irin rahotannin da muka rika samu a ’yan kwanakin nan, haka ya sa mata da dama suke tsoton zuwa gonakinsu su kadai kada a yi musu fyade.

Wani mafarauci a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tuni aka kama wani mutum da ake zargi da hannu a aikata kisa da kuma fyaden.

Ita ma Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin ga ’yan jarida.

Ta ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Mima, kuma yanzu haka yana can a tsare.

Tsofaffin ma’aikatan Gombe 2,204 sun karɓi giratuti N4.2bn

Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja 

Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra