An yi wa wani mai gidan kallo yankan rago a Kaduna

Daga An yi wa wani mai gidan kallo yankan rago a Kaduna A ranar Asabar da ta gabata ne mazauna layin Aminu da ke kusa da tsohon cocin YMCA a Tudun Wada Kaduna suka wayigari cikin tashin hankali saboda samun gawar wani mutum mai suna Musa Aliyu da ke gidan kallo an masa yankar rago.Mutumin […]

An yi wa wani mai gidan kallo yankan rago a Kaduna

Daga An yi wa wani mai gidan kallo yankan rago a Kaduna

A ranar Asabar da ta gabata ne mazauna layin Aminu da ke kusa da tsohon cocin YMCA a Tudun Wada Kaduna suka wayigari cikin tashin hankali saboda samun gawar wani mutum mai suna Musa Aliyu da ke gidan kallo an masa yankar rago.
Mutumin wanda ya jima yana harkar gidan kallon kwallo babu wanda ya san ko su wane ne suka yi masa wannan kisar gilla, illa makwabta sun wayi ne suka tarar da gawarsa a kwance a bakin shagonsa cikin jini.
Wasu da suka ga gawar sun shaida wa Aminiya cewa an sassare shi kafin aka yi masa yankan rago.”Abin babu kyan gani domin na kasa karasawa kusa da wurin domin an sassari gawar sannan aka yanka shi. Jini ya bata wurin da yake kwance,” inji wani matashi da ya ga gawar da bai ambaci sunansa ba.
Akwai masu zargin wani yaronsa da ke duba masa shago da kashe shi, kasancewar tare suke kwana a shagon. An ce tun daga ranar da abin ya faru babu wanda ya san inda yaron yake.
“An ce marigayin ne ya kawo yaron amma babu wanda ya san daga ina ya kawo shi. Tare kuma da yaron suke kwana a cikin shagon har zuwa lokacin da abin ya faru. Sai dai har yanzu ba a ga yaron ba,” inji wani mutum a wurin da abin ya faru.
An ce marigayi Musa ya taba yin aure har yana da da daya, amma wasu sun ce sun rabu da matarsa shi ya sa ya koma kwanan shago a inda yake harkar nuna kwallo.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Aminu Lawan ya ce sun fara bincike domin gano abin da ya faru a ranar.
A wani labarin an tsinci gawar wani jariri a gefen gadar Kogin Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.
Wadanda suka fara gano gawar sun ce wani matashi ne ya gano gawar da safe. “Ya je wucewa ne da safe sai ya ga wani abu a lullube da zani da ya duba sai ya ga gawar jariri ne sabon haihuwa. Daga nan ne sai ya sanar da ’yan bangan unguwar su kuma suka sanar da ’yan sanda.
Sai dai bayan tsawon lokaci da ’yan sintirin suka ga alamar ’yan sandan ba za su zo ba kuma ga shi rana ta soma yi, jama’a na karuwa sai suka binne gawar a nan kusa da kogin,” inji wani mazaunin unguwar wanda bai son a ambaci sunansa.