An yi wa wani manomi yankan rago a Jihar Kaduna

A safiyar Lahadin makon jiya ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa wani manomi mai suna Malam Halliru Tawatsu kisan gilla ta hanyar yi masa yankan rago a gonarsa da ke kauyen Tawatsu a karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna. Wakilin Aminiya wanda ya ziyarci kauyen ya ruwaito […]

An yi wa wani manomi yankan rago a Jihar Kaduna
An yi wa wani manomi yankan rago a Jihar Kaduna

A safiyar Lahadin makon jiya ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa wani manomi mai suna Malam Halliru Tawatsu kisan gilla ta hanyar yi masa yankan rago a gonarsa da ke kauyen Tawatsu a karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Wakilin Aminiya wanda ya ziyarci kauyen ya ruwaito cewa, Alhaji Halliru Tawatsu yana zauna ne a kauyen Samara da ke karamar Hukumar Sabon Gari dan asalin Tawatsu ne, kuma ya yi suna a harkar noman rani da damina da kiwon kifi a Tawatsu.
Marigayin, an ce yana fuskantar matsaloli a tsakaninsa da wasu manoma da bincike ya gano, an sha ganinsa da wasu mutane suna zama don yin sulhu kan filin noma da sauransu.
daya daga cikin jikokinsa da aka sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa an wayigari da shi lafiya, sai ya ce zai je gona kamar yadda ya saba, amma da aka ga bai dawo ba ne sai aka fara tunanin ko ba lafiya.
Ya ce an tafi Tawatsu don a ji halin da yake ciki, inda mazauna kauyen suka ce, lallai ya zo kuma ya tafi gonarsa, sai aka wuce gonar aka duba masallacin da ke ciki, sai aka ga takalminsa na shiga ruwa, rambut, da aka ci gaba da dubawa ne aka samu gawarsa a cikin ruwan da yake kiwon kifi aka fito da shi. Ya ce an ga miyagun sara da makami a jikinsa har shida. Marigayin mai shekara 62 ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya 22.
Babban Jami’in ’Yan sandan yankin Giwa ya tabbatar da faruwar lamarin a inda ya ce sun dukufa bincike don gano wadanda suka yi aika-aikar.