An yi wa wani matashi kisan gilla a Argungu
Ranar Lahadin makon jiya ne aka tsinci gawar wani matashi mai shekara 23 mai suna Musa Abubakar (Shaho) a wani kwararo a Unguwar ’Yar’aduwa da ke garin Argungu a Jihar Kebbi.Wakilinmu wanda ya ziyarci unguwar ya samu zantawa da yayan mamacin mai suna Rufa’i Abubakar wanda ya bayyana masa cewa “Ranar Lahadi da misalin karfe […]
Ranar Lahadin makon jiya ne aka tsinci gawar wani matashi mai shekara 23 mai suna Musa Abubakar (Shaho) a wani kwararo a Unguwar ’Yar’aduwa da ke garin Argungu a Jihar Kebbi.
Wakilinmu wanda ya ziyarci unguwar ya samu zantawa da yayan mamacin mai suna Rufa’i Abubakar wanda ya bayyana masa cewa “Ranar Lahadi da misalin karfe 2:00 bayan na yi alwala ina hanyar zuwa masallaci sai aka aiko daga cikin gidanmu cewa ya je wani kwararo don ya duba kanensa an ce an gan shi kwance cikin jini. Ban yi wata-wata ba na nufi inda aka yi min kwatance, ina zuwa na tarar da gawarsa har ma ya fara kangarewa, daga nan sai na dauko shi a kafadata na nufo gida.”
Ya ce daga nan aka yanke shawarar a sanar ’yan sanda kafin a rufe shi, kuma bayan da ’yan sandan suka zo sai aka dauki gawar zuwa babban asibitin Argungu likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, daga nan sai aka zo aka yi masa wanka aka yi masa jana’iza.
Rufa’i ya ce akwai alamun an yi wa kanen nasa wanda ke sana’ar acaba duka ne saboda hancinsa da bakinsa da kunnuwansa duk suna fitar da jini har zuwa lokacin binne shi, kuma kansa ya kumbura.
Wasu majiyoyi a unguwar sun ta’allaka mutuwar marigayin da fada ko rashin jituwa a tsakaninsa da wani a cikin dakin wani abokinsa mai suna Murtala A. A. Na Maroko inda aka fasa masa ido kuma ya tsiyaye bayan ya mutu kuma sai aka janyo shi aka fitar da shi daga cikin dakin aka yar a waje.
Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi ASP Muhammad Mainagge amma wayarsa a kashe kuma ya tura masa sako amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba amsa.