An yi wa wani yankan rago a Kano
Wasu mutanen da ba san ko su wane ne ba, sun yi wa wani mutum mai suna Adamu Malam Idris yankan rago a Unguwar Tsami a garin Makoda, Jihar Kano. Makasan sun kuma yashe kayan gidan marigayin, kuma suka cinna wuta ga gidansa. Wani makwabcin marigayin mai suna Adamu Usman, ya shaida wa Aminiya cewa […]
Wasu mutanen da ba san ko su wane ne ba, sun yi wa wani mutum mai suna Adamu Malam Idris yankan rago a Unguwar Tsami a garin Makoda, Jihar Kano. Makasan sun kuma yashe kayan gidan marigayin, kuma suka cinna wuta ga gidansa. Wani makwabcin marigayin mai suna Adamu Usman, ya shaida wa Aminiya cewa al’amarin ya faru ne da misalin karfe 3:00 dare ranar Lahadi, inda ya ce mutanen sun je ne a kan babur, kuma har suka yi abinsu suka gama ba a gane ba, sai bayan sun tafi. Ya ce “bayan sun yanka shi sun kai gawarsa ban-dakin suka jefar, sannan suka debe duk kayan gidan, sannan suka cinna wuta a gidan.”
Malam Usman ya ce haushin karnuka a lokacin faruwar abin ne ya sa wasu makwabta suka Ankara, kuma bayan da suka shiga gidan ne, suka tarar da gawarsa cikin jini suka dauke ta zuwa Asibitin dambatta, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa. Malam Usman ya ce “iyayen Adamu sun rasu da dadewa, kuma ba a san wani dan uwansa ba, a garin.” Wasu sun shaida wa Aminiya cewa Malam Adamu mai kimanin shekara 37, ba ya da aure kuma shi kadai yake zaune a gidansa. Kuma yana acaba ne da bayar da bashi ga jama’a.
A yayin da Aminya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya, ya ce, “Jami’anmu sun isa gidan marigayin, kuma sun gano cewa maharan sun yi kokawa da shi kafin su rinjaye shi. Za mu ci gaba da bincike kuma za mu kama mutanen da yardar Allah.”