An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
Wadanda suka mallaki karnuka idan suka “lura suna amai, ko alamar rashin lafiya” su gagauta tuntubar likitan dabbobi.”

Luna, Karyar da ta hadiye safa
Wata karya ta haɗiyi safa 24 da sauran kayan sawa, inda suka maƙale mata a muƙamuƙi- lamarin da ya haifar da yi mata tiyatar ceton rai a Jihar California a Amurka, kamar yadda cibiyar kula da dabbobi ta bayyana.
Wata karya mai suna Luna, jinsin Bernese Mountain da ta shafe wata 7 tana fama da rashin lafiya, sakamakon haɗiye wasu kayayyaki na mamallakinta a ranar 16 ga Fabrairu bayan kamar yadda Cibiyar Ba da Agajin Dabbobi ta Corona ta ce a cikin wani sakon da ta wallafa a Instagaram.
- Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
- Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas
Lokacin da ta fara amai, an garzaya da ita zuwa asibitin dabbobi, inda wani likitan dabbobi ya bude cikinta, ya cire tufafin da ya haifar da toshewar hanjinta.
“Lokacin da ‘yan uwan masu karyar suka lura tana amai kuma tana cikin rashin lafiya mai tsauri, sai suka garzayo da ita wurinmu,” in ji cibiyar.
“Ba tare da bata lokaci ba, yanzu Luna yanzu ta fara kada wutsiyarta!” Ta kara da cewa “karyar tana da tsananin son safa “.
Cibiyar kula da lafiyar dabbobi ta saka hoton safa da aka cire daga hanjin karyar tare da hotunan D-ray na toshewar hanjinta, a cewar kafar Storyful, wanda ya fara gano labarin ceton karyar.

Wasu hotuna sun nuna Luna – tana wasa – cikin farin ciki da kwanciyar hankali a kan gadon asibiti, bayan an yi mata tiyata.
Cibiyar ta yi gargadin cewa, wadanda suka mallaki karnuka idan suka “lura suna amai, ko alamar rashin lafiya” sai su yi sauri su tuntubi likitan dabbobi.”
“Ita wannan karyar ta musamman ce, kuma muna farin cikin samun labarin murmurewarta,” in ji wani sakon da wani ya wallafa.