An yi wa ’yan jarida fashi suna tsakar daukan rahoto kan yawaitar fashi da makami
Sun kwace musu kudi da wayoyi da kuma kyamarar da suke aiki da ita.
Ma’aikatan wani gidan talabijin da suke tsaka da daukar rahoton yawaitar fashi, su ma an yi musu fashi a wani yanayi na ban mamaki.
Wannan lamari ya faru ne a birnin Chicago na kasar Amurka a wata unguwa da ke yammacin birnin da ake kira da West Side.
Wadanda aka yi wa fashin suna aiki ne da gidan talabijin na Unibision mai yada shirye-shiryensa a harshen Sipiniyanci,” in ji jaridar Chicago Sun Times.
Yadda lamarin ya faru shi ne ma’aikatan talabijin din sun isa wani wuri a unguwar suka fito da kayan aiki, inda mai daukar hoto da mai rahoto suka fara daukar rahoto sai wasu motoci biyu suka tsaya a gabansu.
Nan da nan wasu mutane dauke da bindigogi da suka rufe fuskokinsu cikin shigar kayan sanyi suka tsare su tare da yi musu kwacen duk abin suke dauke da su, kamar kudi da wayoyi da sauransu, suka kuma kwace kyamarar da suke aiki da ita, suka shiga motocinsu suka gudu.
Godinez, wani babban jami’in gidan talabijin ya ce, ba za su bayyana sunayen ma’aikatan nasu da aka yi wa fashi a bakin aiki ba.
Ya ce su biyu ne daya dan shekara 28 da mai shekara 42, mai daukar hoto da mai rahoto.
Sun kuma yi haka ne a cewarsu don kada a jefa rayuwarsu a cikin hadari.
“Ina mai tabbatar muku da cewa sunan cikin koshin lafiya kuma suna taimaka wa ’yan sanda wajen bincike,” in ji shi.
Wannan abin da ya faru shi ne na biyu a jerin fashi da makamin da ya faru da ’yan jaridar da ke aiki a garin Chicago.
A baya an kai irin wannan hari ga wani dan jarida mai daukar hoto na kafar labarai ta WLS, a cewar jaridar.