An yi wa ’yan kungiyar asiri afuwa a Jihar Ogun

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, sun yi wa wasu ’yan kungiyar asiri afuwa bayan da suka bayyana tubarsu a fili.  ’Yan kungiyar asirin su 9, wadanda jami’an ’yan sanda suka kame su a kwanakin baya a karamar Hukumar Ewekoro, an kai ga yi musu afuwa ne bayan da suka […]

An yi wa ’yan kungiyar asiri afuwa a Jihar Ogun
An yi wa ’yan kungiyar asiri afuwa a Jihar Ogun

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, sun yi wa wasu ’yan kungiyar asiri afuwa bayan da suka bayyana tubarsu a fili.  
’Yan kungiyar asirin su 9, wadanda jami’an ’yan sanda suka kame su a kwanakin baya a karamar Hukumar Ewekoro, an kai ga yi musu afuwa ne bayan da suka bayyana anniyarsu ta ficewa daga kungiyar. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abudulmajid Ali ya shaida wa Aminiya cewa sun yake shawarar yi wa ’yan kungiyar asirin afuwa ne bayan tattaunawar da suka yi da gwamnan jihar, inda suka yi fatan za su sauya daga mummunar dabi’unsu zuwa dabi’u nagari.
A Larabar da ta gabata ce aka yi wa ’yan kungiyar asirin wankan tsarki, inda Musulmin cikinsu suka yi rantsuwa da Alkur’ani, Kiristoci kuma da littafin Baibul. Bayan sun yi rantsuwar fita daga kungiyoyin asirin sai suka rattaba hannu tare da shan alwashin watsi da munanan dabi’unsu.
A daidai lokacin da ake gudanar da taron, wanda ya gudana a karkashin kulawar kwamishinan ’yan sandan jihar tare da sarakunan gargajiya na karamar Hukumar Ewekoro da shugaban karamar hukumar, shuwagabannin taron sun yi ta kira ga duk wani dan kungiyar asiri da ya bayyana kansa ya tuba, domin a yafe masa. Hakan ne ya sanya aka sami karin mutum uku daga cikin mahalarta taron, suka fito suka bayyana kansu su ma suka tuba.
Shuwagabannin al’ummar sun yi kira ga iyayen yara da su kula da tarbiyar ’ya’yansu. A nasa bangaren, dan majilisar wakilai mai wakiltar karamar Hukumar Ewekoro da Ifo, Isiyaka Ibrahim ya yi alkawarin tallafa wa matasan da suka tuba, domin ingantuwar rayuwarsu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abulmajid Ali, wanda ya bayyana aikace-aikacen ’yan kungiyoyin asiri a matsayin tushen dukannin miyagun ayyuka da kan faru a yankin, ya shaida cewa wannan afuwa ita ce ta karshe a wannan karamar hukuma, domin kuwa duk wanda aka sake kamawa da laifin zai dandana kudarsa.