An yi wa ’yan kwallon Super Eagles ruwan duwatsu a Habasha

Dan kwallon tsakiya a kulob din Najeriya Super Eagles mai suna Nosa Igeibor ya samu rauni a hannunsa na dama a lokacin da magoya bayan kasar Habasha suka yi wa motar bas da ke dauke su ruwan duwatsu akan hanyarsu ta komawa otel din da aka sauke su a ranar Lahadin da ta wuce. Rahoton […]

An yi wa ’yan kwallon Super Eagles ruwan duwatsu a Habasha

Dan kwallon Super Eagles Nosa Igiebor da aka yi wa rauni a hannu a HabashaDan kwallon tsakiya a kulob din Najeriya Super Eagles mai suna Nosa Igeibor ya samu rauni a hannunsa na dama a lokacin da magoya bayan kasar Habasha suka yi wa motar bas da ke dauke su ruwan duwatsu akan hanyarsu ta komawa otel din da aka sauke su a ranar Lahadin da ta wuce.
Rahoton da kafar sadarwar kickoffnigeria.com ta kalato ya nuna, al’amarin ya faru ne jim kadan bayan an kammala wasa a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ta Habasha a ranar Lahadin da ta wuce.
Da yawa daga cikin ’yan kwallon sun sunkuya a cikin motar ce a lokacin da al’amarin ya faru amma kafin Nosa ya ankara gilashin da aka fasa ya yanke shi a hannun dama kuma jini ya rika kwarara babu kakkautawa har sai da Likitansu Ibrahim Gyaran ya yi masa magani.
Jim kadan da tashi wasan ne, bayan da Najeriya ta lallasa Habasha da ci 2-1 magoya bayan Habasha suka fara yunkurin ci wa ’yan kwallon Najeriya mutunci da hakan ta sa jami’an tsaro suka umarci ’yan kwallon da kada su kuskura su bar filin a wannan lokaci.
Jim kadan bayan sun samu sukunin fita ne ashe wasu daga cikin magoya bayan sun yi musu kofar-rago a kan hanyarsu ta komawa masaukinsu inda suka rika jifansu da duwatsu don nuna bacin ransu a kan rashin nasara da suka samu a wasansu da Najeriya.
Mataimakin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta kasa Cif Mike Umeh ya ce tuni hukumarsa ta kai koke ga Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) a kan wannan al’amari kuma yanzu haka suna sauraron abin da zai biyo baya.
A ranar 16 ga watan gobe ne ake sa ran kasar Habasha za ta ziyarci Najeriya a wasa karo na biyu kafin a tantance kasar da za ta haye gasar cin kofin duniya da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Sai dai Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta bada tabbacin samar da tsaro da kuma kariya ga ’yan kwallon Habasha a lokacin da za su ziyarci garin Kalaba a wasa karo na biyu.

…Najeriya za ta yi wasan sada zumunta da Italiya

A ranar 18 ga watan gobe ne ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kara da ta Italiya a wasan sada zumunta da zai gudana a birnin Landan.
Wasan, za a yi shi ne a matsayin shirye-shiryen tafiya gasar cin kofin duniya ga kasashen biyu da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Za a yi wasan ne kwana biyu  bayan Super Eagles ta kara da kungiyar kwallon kafa ta Habasha a wasa zagaye na biyu a Kalaba, wanda zai gudana a ranar 16 ga watan Nuwamban wannan shekara.
 Ita ma Italiya ta bayyana cewa za ta kara da kara da kasar Jamus  kwana biyu kafin ta hadu da Najeriya a wasan sada zumuntar.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce, baya ga Italiya, tana sa ran kungiyar Super Eagles za ta kara da kasar Jordan a ranar 28 ga watan nan da muke ciki a wasan sada zumunta.
Sai dai a wasan da Najeriya za ta kara da Jordan, za a yi amfani da ’yan kwallon da ke wasa a cikin gida ne a shirinsu na tunkakar gasar cin kofin kalubale na matasan Afirka da zai gudana a watan Janairu a kasar Afirka ta Kudu.
Wannan shi ne karo na farko da Najeriya za ta hadu da Jordan a wasan kwallo a kowane mataki.
Tuni hukumar kwallon kafa ta kasa NFF shaidawa manema labarai cewa a wannan makon ake sa ran fitar da sunayen ’yan kwallon da za a gayyato don su fara samun horo a Abuja kafin su wuce Amman da ke Jordan don gudanar da wasan sada zumuntar.
Rabon da Najeriya ta hadu da Italiya tun a gasar cin kofin duniya da ya gudana a shekarar 1994 a Amurka inda da kyar da jibin goshi Italiya ta doke Najeriya da ci 2-1a lokacin da Najeriya ke ji da ’yan kwallo irin su Rashidi Yekini da Daniel Amokachi da sauransu.