An yi wa ‘yan majalisar Swaziland dokar sakin aure

Shugabar Majalisar Dattijai na kasar Swaziland ya umarci ’yan majalisar kasar da kada su kuskura su saki matansu, don yin hakan cin mutunci ne ga Sarkin kasar mai matan aure da yawa, baya ga cewa ya yi dokar cewa mutuwa kadai ke raba auren al’ada. Gelane Zwane, Shugabar wannan babbar majalisa, a wannan kasa daya […]

An yi wa ‘yan majalisar Swaziland dokar sakin aure
An yi wa ‘yan majalisar Swaziland dokar sakin aure

Shugabar Majalisar Dattijai na kasar Swaziland ya umarci ’yan majalisar kasar da kada su kuskura su saki matansu, don yin hakan cin mutunci ne ga Sarkin kasar mai matan aure da yawa, baya ga cewa ya yi dokar cewa mutuwa kadai ke raba auren al’ada.

Gelane Zwane, Shugabar wannan babbar majalisa, a wannan kasa daya tilo da ke karkashin mulkin sarkin gargajiya, ta bayyana cewa, akwai bukatar ’yan majalisa su kasance abin doka misali ga matasan kasa, sannan ta gargade su game da kokarin shawo kan sha’awarsu.
Sannan ta shawarcimata ’yan majalisa da su guji yin amfani da mukamin su wajen yin “rashin biyayya” ga mazan su na aure, ta kuma ce su daina kallon tsiraicin mata ’yan uwansu.
Wannan doka da Zwane ta ce ta fi shafar mata, ta biyo bayan ikrarin Sarki Mswati III ne, wanda a farkon wannan shekarar ya furta cewa ‘mutuwa kadai ke iya raba auren da aka kulla kan tafarkin al’adun gargajiya, duk da cewa al’adar Swazi ta yarda a raba aure.
“Duk sa’adda mutane suka zama ’yan majalisar, ana bibiyar rayuwarsu ta bayan fage,” inji ta. “Muna kokarin hana sakin aure, saboda kamata ya yi ’yan siyasa su kasance masu kyawawan dabi’u, ta yadda za su zama abin koyi ga na baya,” a cewarta.
Zwane ta kaddamar da dokar ne a wajen wani taron kara wa juna sani da aka shirya wa ’yan majalisa. Don haka ’yan majalisar da ke da karar sakin aure a kotuna, sai su dakata har sai wa’adin mulkinsu ya kare, nan da shekara ta 2018.
Ta ce, akwai rashin fahimta cewa “matan da ke rike da mukaman siyasa suna wulakanta mazajensu har ma su sake su.”
Ta kuma yi tuni ga ’yan majalisar,musamman mata,cewa “a lokacin da suke rike da mukaman siyasa, kuma suke fama da yamutsin sakin aure, hakan na iya zama batanci ga hukuma,” inda ta yi nuni da sarkin kasar.
Shugabar majalisar ta karkare bayananta, inda ta roki maza da su daina kulla wata alaka ta daban da mata 95 da ke rike da mukamai a majalisar.