An yi wa ’yan NYSC ƙarin alawus zuwa N77,000
Ƙarin albashin da aka yi ya fara aiki ne daga watan Yulin shekarar 2024 da muke ciki
Gwamnatin Tarayya ta yi wa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ƙarin kuɗin alawus ɗinsu na wata-wata zuwa Naira 77,000.
Hukumar Kula da Alabshi ta Ƙasa ta bayyana cewa ƙarin ya fara ne daga watan Yulin shekarar 2024 da muke ciki.
An yi wa masu yi wa ƙasa hidima ƙarin kuɗin ne daga Naira 33,000, domin dacewa da sabon mafi ƙarancin albashi N70,000 da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi.
Wannan na ƙunshe ne w cikin sanarwar da shugaban hukumar kula da alabshi ta ƙasa, Ekpo Nta, ya fitar a ranar Laraba.
- Bidiyon Tsiraici: Hafsat Baby ba ta hannunmu —Hisbah
- NAJERIYA A YAU: Shin Ƙarin Kuɗin Ruwa Zai Farfaɗo Da Tattalin Arzikin Najeriya?
Gabanin haka, a yayin ziyarasa, Darakta-Janar na hukumar NYSC, YD Ahmed, ya buƙaci ƙarin albashi ga nasu yi wa ƙasa hidima.
Ya bayyana cewa ƙarin zai ƙara musu azama wajen hidima wa ƙasarsu.