An yi wa ’yar shekara 9 fyaɗe an kashe ta a Jos
Ina cikin ƙunci a halin yanzu. Duk wanda ya aikata wannan lamari sai ya girbi irin abin da ya shuka saboda ba zan yafe ba.
Ana fargabar cewa an kashe wata ’yar shekara tara bayan an yi mata fyaɗe a Unguwar Layin Isiyaku Gwamna da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.
Lamarin kamar yadda iyayen yarinyar suka tabbatar ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Alhamis yayin da aka aike ta sayen man gyaɗa, inda aka tare ta a hanya kuma mai aukuwa ta auku.
- Falalar da ke tattare da azumin watan Ramadan
- Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga shugabancin Hukumar Kula da Almajirai
Wata yayar wadda lamarin ya shafa da aika ta bi sahun kanwarta, ta bayyana yadda ta riski gawar ’yar uwarta an rataye a wani kango.
“An ce na bi sahunta bayan ta shafe sa’o’i ba ta dawo gida ba daga aiken da aka yi mata ba.
“Sai na riƙa bin duk hanyar da na san cewa ta nan za ta bi wajen sayen man gyaɗar da aka aike ta siyowa.
“Ina tsakar tafiya sai na mayar da abin wasa ina kira sunanta — wance, wance— sai kwatsam ina cikin waiwaye na hango ta rataye cikin wani tsohon gini.
“Daga nan na ruga gida na kirawo mahaifinmu wanda ya zo ya kwanto ta aka tafi da ita gida.
Mahaifiyar yarinyar da lamarin ya shafa, ta bayyana mutuwar ’yarta a matsayin abin takaici, tana mai kiran hukumomin tsaro su gudanar da bincike domin kama duk wani mai hannu a aika-aikar.
Mahaifiyar ta bayyana cewa, “wannan abu ya taba ni sosai, ina cikin ƙunci a halin yanzu. Duk wanda ya aikata wannan lamari sai ya girbi irin abin da ya shuka saboda ba zan yafe ba. Shi ma a kashe shi. A bi wa ’yata hakkinta.
Dangane da abin da ba za ta taba mantawa da marigayiyar ba, mahaifiyar ta ce za ta yi kewar yadda duk da ƙarancin shekarun ’yarta, amma ta san ta yi wa iyayenta addu’a da neman tabarrakinsu kan duk abin da za ta yi.
Su ma dai mazauna da sauran masu bayyana alhini sun buƙaci hukumomin tsaro da su gaggauta bankaɗo duk masu hannu a wannan aika-aikar domin fuskantar hukuncin da zai zama izini ga sauran al’umma.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da ingancin rahoton da cewa ”’yan sanda na sane da lamarin.
“Mun kama mutum ɗaya yanzu haka kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.”