An yi wani matashi yankan rago

A karshen makon jiya ne al’uumar Unguwar danbare a karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano suka tashi da alhinin rasuwar wanidan unguwar mai suna Hafizu Mahmud inda suka tsinci gawarsa cikin jini a wani kango da ke makwabtaka da gidansa.Malam Ahmad Sani makwabcin marigayin ya shaida wa Aminiya cewa yara ne da ke wasan kwallo a […]

An yi wani matashi yankan rago
An yi wani matashi yankan rago

A karshen makon jiya ne al’uumar Unguwar danbare a karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano suka tashi da alhinin rasuwar wanidan unguwar mai suna Hafizu Mahmud inda suka tsinci gawarsa cikin jini a wani kango da ke makwabtaka da gidansa.
Malam Ahmad Sani makwabcin marigayin ya shaida wa Aminiya cewa yara ne da ke wasan kwallo a kango suka ci karo da gawar marigayin da misalin karfe 5:00 na yamma inda suka sanar da jama’ar unguwa. “Lokacin da muka shiga cikin kangon mun iske shi kwance cikin jini. An yanka wuyansa, sannan a gefe guda ga reza ga kuma hular marigayin a ajiye,” inji shi.
Kafin rasuwarsa marigayi Hafizu yana gudanar da harkar kasuwanci a Kasuwar Kwari da ke birnin Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ASP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rundunarsu ta fara bincike don gano wadanda suka yi wannan aika-aika. “Muna bincike don gano wadnda suka aikata wannan kisan gilla, insha Allahu hakkin rai ba zai bar su su sha ba da sannu za su zo hannunmu,” inji Majiya.