An yi wasan kwallon sada zumunci a tsakanin tsofaffin ’yan wasa a Jihar Katsina

Tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da suka fito daga kungiyoyin kwallon kafa daban-daban daga fadin Jihar Katsina sun tuna baya a ranar Lahadin da ta gabata a tsohon filin wasa da ke cikin garin Katsina. Tsofaffin ‘yan wasan wadanda suka zanta da manema labarai bayan kammala wasan sun ce,wasun su sun wuce shekara 35 zuwa […]

An yi wasan kwallon sada zumunci a tsakanin tsofaffin ’yan wasa a Jihar Katsina
An yi wasan kwallon sada zumunci a tsakanin tsofaffin ’yan wasa a Jihar Katsina

Tsofaffin ‘yan wasan kwallon kafa da suka fito daga kungiyoyin kwallon kafa daban-daban daga fadin Jihar Katsina sun tuna baya a ranar Lahadin da ta gabata a tsohon filin wasa da ke cikin garin Katsina. Tsofaffin ‘yan wasan wadanda suka zanta da manema labarai bayan kammala wasan sun ce,wasun su sun wuce shekara 35 zuwa 40 rabon su da kwallo sai a wannan rana.

Kamar yadda wanda ya shirya wannan wasa, tsohon dan wasa Alhaji Sani Lawal BK ya ce, sun shirya wannan wasan ne don taya Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari tare da Mataimakinsa Alhaji Mannir Yakubu don taya su murna akan yadda aka gudanar da Azumin watan Ramadan da bukukuwan karamar salla lafiya a matsayinsu na sabbin shugabannin da suke mulki da suka fito daga wata jam’iyya bayan shekaru 16 da jam’iyar da ta shude tana mulki tare kuma da farfado da zumuncin da suka dauki dogon lokacin da ba su hadu don sadar da shi ba ta fuskar wasanni.
Sani Lawal ya kara da cewa sun kasu gida biyu ne wato sashen gwamna da kuma na mataimakinsa inda suka fafata. Ya ce,duk da wannan shi ne karon farko da tsofaffin ‘yan wasan suka yi irin wannan wasa don sada zumunci, wasan na da zimmar kara habaka wasannin motsa jiki a fadin jihar Katsina. “In kuka duba za ku ga wasu daga cikinmu za a yi zaton ba za su iya komai ba amma kun ga yadda suke taka leda cikin nishadi da annashuwa. Mun yi haka ne don nuna wa na baya muhimmancin wasan motsa jikin da kuma yadda yake kawo jituwa da kuma sada zumunci a tsakanin ‘yan wasan da ke fitowa daga sassa daban-daban wanda hakan ke kara kawo zaman lafiya”.
Shi kuwa Mataimakin gwamnan Jahar Katsina Alhaji Mannir Yakubu wadanda ya kasance babban bako a wajen wasan ya ce gwamnatinsu za ta yi iya kokarinta nwajen habaka wasannin motsa jiki a fadin jahar. Mataimakin gwamnan wanda ya jinjina wa tsofaffin ‘yan wasan da suka shirya wannan wasa na sada zumunci tare da taya su murna. Ya shawarci ‘yan wasan da su yi kokarin shirya gasa a tsakanin ‘yan kulob-kulob da ke fadin jihar domin fitar da kwararrun ‘yan wasan da za su rika wakiltar jihar a fannoni daban-daban na wasanni ba sai na kwallon kafa ba. An dai tashi wasan bangaren mataimakin Gwamna ne suka yi nasara da ci daya da nema.

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja