An yi ’yar jefe-jefe da hanjin aladu a zauren Majalisar Taiwan

Wakilan Majalisar Dokokin Taiwan sun  bai wa hammata iska a zauren majalisar kan wani kudirin dokar da zai bai wa kasar Amurka damar shiga da naman aladu da na shanu zuwa kasar Taiwan, wanda hakan bai yi wa wadansu ’yan majalisar dadi ba, inda suka fara bai wa hammata iska tare da watsa hanjin aladu […]

An yi ’yar jefe-jefe da hanjin aladu a zauren Majalisar Taiwan

Yadda aka rika watsa hanjin aladu a Majalisar Taiwan

Wakilan Majalisar Dokokin Taiwan sun  bai wa hammata iska a zauren majalisar kan wani kudirin dokar da zai bai wa kasar Amurka damar shiga da naman aladu da na shanu zuwa kasar Taiwan, wanda hakan bai yi wa wadansu ’yan majalisar dadi ba, inda suka fara bai wa hammata iska tare da watsa hanjin aladu a cikin zauren majalisar.

Firimiyan Taiwan, Mista Su Tseng-chang ne koyaushe yake ba da rahoton tsare-tsaren dokokin da aka shirya ga ’yan majalisa a kowace safiyar Juma’a kan dokar naman aladun, yayin da bangaren jam’iyyun adawa na Nationalist Party, wanda aka fi sani da KMT suka dakatar da shi lokacin da ya so yin bayani a zauren majalisar, inda suka ajiye wasu jakunkuna dauke da wasu sassan jikin aladun da aka yanka.

Wadansu ’yan majalisa daga jam’iyya mai mulki ta Democratic Progressive Party (DPP) sun yi yunkurin dakatar da su amma abin ya ci tura har ta kai ga ba hammata iska a majalisar.

Wani dan majalisa daga Jam’iyyar DPP ya kama wani takwaransa na Jam’iyyar KMT da  kokuwa a zauren majalisar.

A watan Agustan bana ne Shugaban Kasar, Mista Tsai Ing-wen’s ya dakatar da shiga da naman aladu da na shanu cikin kasar daga Amurka, wannan ne mataki na farko da kasar ta kulla yarjejeniya huldar kasuwanci da Amurka, an dai kafa dokar ce tun a watan Janairun da ya gabata, inda aka kara tsawaita dokar.

Wannan muhawarar ta janyo takun-saka a tsakanin jam’iyyun biyu mai ci da ta adawa da kuma mutanen kasar.

Sabuwar dokar ta bai wa Amurka damar shiga da naman aladu da naman saurandabbobi, ta sa manoma za su fara sayen magungunan da za su sanya dabbobinsu su kara girma.

A kwanakin baya ne wadansu mutanen kasar a garin Taipei suka gudanar da zanga-zanga kan dokar.

Naman aladun Amurka na daga cikin kashi mafi karancin da mutanen Taiwan ke saya idan aka kwatanta da na kasashen da ke da manyan tekuna kuma suke shigar da naman dabbobi zuwa kasar Taiwan.

Amma Jam’iyyar Nationalist Party ta yi kokarin fadakar da magoya bayanta kan rashin samun nasarar da jam’iyyar ta yi a zaben da aka yi.

“A lokacin da ba jam’iyyar mai mulki bace a kujera, ta ki amincewa da sayar da naman aladun Amurka a kasar, amma  yanzu ita ce ke kan gaba wajen goyon bayan sayar da naman aladun Amurka a kasar,” inji wani dan majalisa daga Jam’iyyar KMT, mai suna Lin Wei-chou wanda ya jagoranci ayarin ’yan majalisar ga yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da dokar a ranar Juma’a.

’Yan majalisar sun sanya riguna masu dauke da rubutun rashin amincewa a sayar da naman dabbobin da ake shigo da su daga kasashen waje zuwa Taiwan.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro