An yi yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso

Shekara guda bayan ya ƙwace mulki da karfin soji a Burkina Faso, an yi yunkurin kifar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore

An yi yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso

Jagoran mulkin Sojin Burkina Faso, Ibrahim Traoré. (Hoto: AFP)

Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta daƙile yunƙurin yi mata juyin mulki, shekara guda bayan shugaban ƙasar, Kyaftin Ibrahim Traore ya hau mulki ta hanyar hamɓarar da gwamnatin baya.

Gwamnatin Kyaftin Traore ta ce a ranar Talata wasu sojoji suka yi yunƙurin hamɓarar da ita, amma ta damke su.

Karo na biyu ke nan cikin mulkinsa na shekara guda da gwamnatinsa ta sanar da nasararta wajen daƙile yunƙurin kifar da ita.

“Abin takaici sojojin da suka yi rantsuwa za su ƙare ƙasarsu sun ɗauki hanyar jefa ƙasar cikin bala’i,” in ji sanarwar gwamnatin ta gidan talabijin na ƙasar.

Bayan sanarwar da kira magoya bayan Traore su kare Burkina Faso ne dubban al’ummar ƙasar suka fito kan titunan birnin Ouagadougou a daren suna jaddada goyon baya gare shi.

Hukumar leken asirin kasar ta ce tana binciken sojojin da suka yunkurin juyin mulkin, tare da neman sauran masu hannu a ciki ruwa a kallo.

Wannan na zuwa ne bayan a watan hukumar ta sanar da cafke wasu sojoji da tsoffin ke aiki a ƙarƙashinta kan zargin tattara bayanai ta bayan fage da kuma bibiyar motsin Kyaftin Ibrahim Traore da manyan jami’an gwamnatimsa.

Wata takwas kafin nan, gwamnatin Traore ta sanar da daƙile yunƙurin kifar da ita a watan Disamban 2022, wata bayan ya yi nasa juyin mulkin.

A lokacin ne gwamnatinsa ta sanar da cafke wasu fararen hula da sojoji ƙarƙashin jagorancin Laftanar-Kanar Emmanuel Zoungrana.

Yunkurin juyin mulkin ranar 26 ga watan Satumba shi ne na uku cikin shekara biyu ƙasar, kuma shekara guda bayan hawan mulkim Traore.

A rana 30 ga watan Satumba 2022 ne ya yi juyin mulki, wata takwas bayan wani juyin mulkin a kasar.

A cikin wata uku da suka wuce an samu yunkurin juyin mulki a Afirka inda na Nijar da Gabon (Agusta)  suka yi nasara, sai na Burkina Faso da aka dakile.

Masu juyin mulkin sun bayyana cim rashawa da gazawar gwamantin baya wajen yakar ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi a matsayin dalilinsu na ƙwace mulkin.

Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 481 suka kama 741 a wata guda

Yau za a yi jana’izar Janar Lagbaja

NAJERIYA A YAU: Shirin Da Masu Ruwa Da Tsaki Suka Yi Kan Zaben Ondo.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu