An yi zaben Laberiya cikin lumana
Zaben kasar Labariya ya wakana cikin lumana, kamar yadda rahotanni ke nunawa. Wannan shi ne karo na uku da za a yi zabe a kasar tun bayan yakin babasar kasar, inda za su zabi sabon shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya. An fafata zaben ne tsakanin ’yan takara 20 wadanda ke son maye gurbin shugaban […]

Zaben kasar Labariya ya wakana cikin lumana, kamar yadda rahotanni ke nunawa.
Wannan shi ne karo na uku da za a yi zabe a kasar tun bayan yakin babasar kasar, inda za su zabi sabon shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya.
An fafata zaben ne tsakanin ’yan takara 20 wadanda ke son maye gurbin shugaban kasa mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf, wadda ita ce mace zababbiyar shugaban kasa ta farko a yankin Afirka.
Daga cikin wadanda ake sa ran za su lashe zaben akwai tsohon dan wasan kwallon kafar kasar sanata George Weah, mataimakin shugaban kasar na yanzu Joseph Boakai,tsohon shugaban ’yan tawayen kasar Yarima Johnson da kuma wata Macdella Cooper.
Haka kuma akwai ’yan takara 986 da suke neman kujera a Majalisar Tarayyar kasar mai kujeru 73. Sannan kuma an tantance mutane 2,183,683, sannan kuma an samu rahoton cewa mutane da yawa son fito domin kada kuri’arsu.
Ba za mu amince da sakamakon zaben ba- Jam’iyyar Liberty
Jam’iyyar Liberty, wanda dan takararta Charles Brumskine ke wadanda wasu ke sa ran zai iya samun nasara a zaben ta bayyana cewa ba za ta amince da sakamakon zaben ba, inda ta ce za ta kotu matukar aka fada samakon zaben.
“Muna kira ga Hukumar Zabe da ta tsaya da sanar da sakamakon zaben. Mun gano abubuwa da dama da aka yi ba daidai ba, idan kuma ba a tsaya ba, to za mu je kotu bayan an kammala sanar da sakamakon zaben,” inji shugaban jam’iyyar Benjamin Sanbee.
A wani bangaren kuma, tuni wasu suka fara taya Geroge Weah murnar lashe zaben, bayan an samu labarin cewa shi ne ke kan gaba a kuri’u duk da cewa ba a samu ingantaccen labarai a kan hakan ba.
A lokacin da ake hada wannan labarin dai ba a riga an sanar da wanda ya lashe zaben ba.