An yi zanga-zanga a Beijing kan bacewar jirgin Malaysiya

Yan uwan wadanda ke cikin jirgin saman Malaysia da ya bace sun gudanar da wata zanga-zanga a wajen Ofishin Jakadancin Malaysia da ke birnin Beijing inda suka bayyana rashin gamsuwarsu da yadda kasar Malaysia ta gudanar da aikin neman jirgin wanda galibin fasinjojinsa 239 ‘yan kasar China ne.Wannan na zuwa ne bayan Firaministan Malaysia Najib […]

An yi zanga-zanga a Beijing kan bacewar jirgin Malaysiya

A relative (C) of passengers on the missing Malaysia Airlines flight MH370 cries as she participates in a protest outside the Malaysian embassy in Beijing on March 25, 2014. Scores of angry relatives of the Chinese passengers aboard Flight MH370 set out on a protest march to the Malaysian embassy in Beijing on March 25 […]

Yan uwan wadanda ke cikin jirgin saman Malaysia da ya bace sun gudanar da wata zanga-zanga a wajen Ofishin Jakadancin Malaysia da ke birnin Beijing inda suka bayyana rashin gamsuwarsu da yadda kasar Malaysia ta gudanar da aikin neman jirgin wanda galibin fasinjojinsa 239 ‘yan kasar China ne.
Wannan na zuwa ne bayan Firaministan Malaysia Najib Razak ya bayyana cewa bayanai da aka samu daga tauraron dan Adam sun tabbatar da cewa jirgin ya fada teku. Ya ce “ Ina mai matukar bakin cikin sanar da ku cewa daga sabbin bayanai da muka samu jirginnan da ya bace mai inkiyar MH370 ya fada  kudancin tekun Indiya ne kuma wannan na nufin sai mu dauki dangana, aikin neman jirgin ya zo karshe ke nan.” Inji shi
Koda jin wannan sai ‘yan uwan wadanda ke cikin jirgin da ke China suka bazama kan tituna birnin Beijing don isa Ofishin Jakadancin Malaysia, hakan ya haifar da arangama tsakaninsu da ‘yan sanda birnin. Amma masu zanga-zangar ba su fasa bayyana rashin gamsuwarsu da bayanai firaministan da kuma ma yadda a cewarsu kasar ta Malaysia ke ci gaba da yin rufa-rufa kan batar jirgin.
A bangare guda kuma kasar China ce da kasar Australia ke ci gaba da shan alwashin cewa ba za su taba gajiya wa ba a aikin neman jirgin.