An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna

Al’ummar yankin sun roƙi gwamnatin Kaduna ta kai musu ɗauki kafin a ƙarar da su.

An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna

Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu.

Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Sun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu.

Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu ba babbaka, tare da sace mutum ɗaya daga ƙauyen.

“Ba mu da kwanciyar hankali kwata-kwata.

“’Yan bindiga suna yawan kawo mana hari a duk lokacin da suka ga dama. Gwamnati da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki kafin mu ƙare,” in ji shi.

Wani mazaunin yankin ya ce matsalar tsaro a Kachia ta kai ga mutane ba sa iya zuwa gonakinsu ko barci cikin kwanciyar hankali.

“Gwamnati ta ce ta yi sulhu da ‘yan bindiga, amma kullum ana kashe mu a Kachia.

“Mutane da dama na cikin daji suna shan wahala kan laifukan da ba su san komai a kansu ba,” in ji shi cikin fushi.

Masu zanga-zangar sun ce ’yan bindiga sun mayar da yankin filin daga, lamarin da ya sa suka tsinci kansu cikin tsananin fargaba da damuwa.

“Ba ma iya zuwa gona, alhali yawancinmu da noma muka dogara,” in ji wani daga cikin masu zanga-zangar.

“Ba ma iya yin barci cikin kwanciyar hankali. Ana so a ƙarar da mu ne?”

Zanga-zangar ta biyo bayan hare-hare da yawaitar sace-sacen mutane a Ƙaramar Hukumar Kachia.

Ƙauyuka irin su Gadanji, Ungwan Wage, Ungwan Alhaji, Agunu Dutse, Maro da Ungwan Dauje na fama da hare-haren ’yan bindiga ba dare ba rana.

Mazauna yankin sun ce duk da kiraye-kirayen da suke yi ga mahukunta, babu wani matakin tsaro da aka ɗauka domin kare su daga hare-haren.

A halin da ake ciki, mazauna yankin na ci gaba da roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo musu ɗauki domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran waya ba.

Ga hotunan yadda zanga-zangar ta gudana:

Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta

Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa

An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna

Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC