An yi zanga-zanga kan kisan wasu mutum 10 a Benuwai

Wasu da dama sun ji rauni, yayin da wasu kuma suka tsere suka bar muhallansu.

An yi zanga-zanga kan kisan wasu mutum 10 a Benuwai

Mazauna Ƙaramar Hukumar Otukpo da ke Jihar Benuwai, sun yi zanga-zanga, biyo bayan kashe wasu mutum 10 da ’yan bindiga suka yi.

An yi zanga-zangar ne a ranar Lahadi, biyo bayan wasu hare-hare a wasu yankuna biyu na Ƙaramar Hukumar.

Maharan sun fara kai hari ƙauyen Akpachi da ke yankin Ugboju da yammacin ranar Asabar, inda suka kashe manoma biyu.

Daga baya sun sake kai hari Otukpo-Nobi da sanyin safiyar ranar Lahadi, inda suka kashe wasu mutum takwas, ciki har da mata da yara.

Shaidu, sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne tsakanin ƙarfe 3 zuwa 5 na Asuba, lokacin da yawancin mazauna yankin ke barci.

Mutane da dama sun jikkata, yayin da wasu mazauna yankin suka tsere daga gidajensu saboda fargaba da zulumi.

Mazauna yankin sun nuna fushinsu ta hanyar kai gawarwakin waɗanda aka kashe zuwa fadar Och’Idoma, inda suka buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin inganta tsaro a yankin.

Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya yi Allah-wadai da kisan, inda ya umarci jami’an tsaro da su ƙara sintiri, su kama waɗanda suka kai harin tare da tabbatar da tsaron waɗanda abin ya shafa.

Sanata Abba Moro, shi ma ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda ya yi ga gwamnati da jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen yawaitar hare-hare a yankin.