An yi zanga-zanga kan yunkurin mayar da mafi karancin albashi hannun Gwamnoni a Kano
Idan dai kudurin ya zama doka, kowacce jiha ce za ta rika yanke abin da za ta biya ma’aikatanta a matsayin mafi karancin albashi
Kungiyoyin kwadago a jihar Kano ranar Laraba sun mamaye ginin harabar Majalisar Dokokin Jihar domin nuna rashin amincewarsu kan yunkurin da Majalisar Dokoki ta Tarayya ke kokarin yi na mayar da yanke mafi karancin albashi a hannun jihohi.
Idan dai kudurin ya zama doka, kowacce jiha ce za ta rika yanke abin da za ta biya ma’aikatanta a matsayin mafi karancin albashi, lamarin da ’yan kwadagon suka ce babbar barazana ce a gare su.
- ’Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban kwadago na Taraba
- Ma’aikata na zanga-zanga kan karancin albashi a Majalisar Tarayya
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen jihar ta Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir ya ce, “Yin hakan tamkar ba Gwamnoni damar mayar da kasar baya ne inda ma’aikata suke zama kamar bayi.
“Idan aka ba Gwamnonin wuka da nama, na tabbatar za a yi ta samun matsala a alakar gwamnati da sauran kungiyoyinmu na ’yan kwadago,” inji shugaban na NLC.
Daga nan sai ya roki zauren majalisar da ya yi fatali da kudurin da zarar ya zo gabansu domin jin dadin ma’ikatan.
Kwamared Minjibir ya kuma ce tuni kungiyoyin suka kammala shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a dukkan jihohi 36 da Abuja domin nuna Allah-wadansu da kudurin, lamarin da ya ce shine zai kasance mataki na farko a fafutukar da suke yi ta kwato wa kansu ’yanci.
Kazalika, shugaban ya roki Gwamnatin Tarayya da ta amince da bayar da ’yancin cin gashin kai wajen samar da kudade ga Majalisun Dokokin Jihohi kamar yadda gwamnati mai ci ta yi alkawari a baya.
Da yake mayar da jawabi a gaban ’yan kwadagon, Kakakin Majalisar ta Kano, Hon. Hamisu Ibrahim Chidari ya ba su tabbacin cewa majalisar ba za su taba yin abinda zai kuntatawa ma’aikatan ba, kuma za su yi duk mai yuwuwa wajen ganin cewa kudurin bai kai ga gaci ba.
A makon da ya gabata ne dai dan majalisa mai wakiltar mazabar Sabon Gari daga jihar Kaduna a zauren Majalisar Tarayya, Garba Datti Muhammad ya gabatar da kudurin bukatar mayar da mafi karancin albashin hannun gwamnonin kuma tuni kudurin ya tsallake karatu na daya da na biyu.
Kungiyoyin dai da suka hada da na NLC da TUC da na fararen hula sun rika rera wakoki da daga kwalaye dake dauke da rubuce-rubucen nuna kin jinin yunkurin.