An yi zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a White House
Masu zanga-zanga sun yi dafifi a fadar White House ta kasar Amurka domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da yankin Gaza.
Masu zanga-zanga sun yi dafifi a fadar White House ta kasar Amurka domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da yankin Gaza.
Taron masu zanga-zangar da suka yi ta daga wake-wake tare da daga kwalayen goyon bayan Falasdinawa da ’yancin kasar Falasdinu, sun Allah-wadai da tsarin diflomasiyyar Amurka da ke goyon bayan Isra’ila.
Daruruwan mutanen sun gudanar da zanga-zangar ce bayan Amurka ta bayyana cewa tsokana ce harin da kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta kai wa Isra’ila a ranar Asabar.
Sai dai masu kare ’yanci sun zargi Isra’ila da mamaye filaye da kuma yin haramtattun gine-gine a wuraren da ta mamaye a Gaza a cikin watannin da uska gabata.
A ranar Asabar mayakan Hamas suka kutsa yankin Isra’ila, inda suka hallaka yahudawa sama da 700 suka yi garkwua da wasu sama da 1oo, ciki har da sojoji.
Daga bisani Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar hare-hare da jirage, inda ta kashe Falasdinawa sama da 570