An yi zanga-zangar goyon bayan masoya a Yemen

An yi zanga-zangar goyon bayan masoya a kasar Yemen, inda mutane suka yi cinciridon nuna goyon baya ga Huda al-Niran ‘yar Saudiyya da masoyinta Muhammad Tahar Arafat dan kasar Yemen. Al’umma ta taru don nuna oyon bayan a taimaka musu su yi aure, duk da cewa Hukumomin Saudiyya ba su amince ba, har ma sun […]

An yi zanga-zangar goyon bayan masoya a Yemen

Huda da ArafatAn yi zanga-zangar goyon bayan masoya a kasar Yemen, inda mutane suka yi cinciridon nuna goyon baya ga Huda al-Niran ‘yar Saudiyya da masoyinta Muhammad Tahar Arafat dan kasar Yemen. Al’umma ta taru don nuna oyon bayan a taimaka musu su yi aure, duk da cewa Hukumomin Saudiyya ba su amince ba, har ma sun bukaci a dawo musu da Huda gida.
Hukumar Majalisar dinkin Duniya Mai kula da ’Yan gudun Hijira, ta amince ta bai wa wata budurwa mafaka a kasar Yemen, bayan da ta tsallaka cikin kasar, ba bisa ka’ida ba, ta kuma ki bin umarnin iyayenta, don kawai ta hadu da masoyinta.
Budurwar, ’yar shekara 22, mai suna Huda al-Niran, ta roki kotun kasar Yemen ta kyaleta ta zauna a kasar don ta auri masoyinta, Arafat Muhamamd Tahar dan shekara 25.
Wadannan magoya baya sun samu dimbin magoya baya, wadanda suka yi cincirindo a kofar kotun kasar Yemen, suna cewa: “Mu dukanmu Huda sunanmu.” Huda dai ta ki amincewa da lauyan da ofishin jakadancin Saudiyya ya bat a, don gudun kada a mayar da ita gida.
Lauya Abdel Rakib al-kadi, ya bayyana cewa Gwamnatin Sana’a’a na shan matsin lamba daga Saudiyya kan lallai a dawo da Huda gida. Masu sharhi kan wannan al’amari suna kwatanta soyayyar Huda da Tahar, da labarin masanin adabin Turancin Ingilishi Shakespears na Romeo and Juliet.Dandazon magoya bayan Arafat da Huda a kotun Yemen

 

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan