An yi zanga-zangar kashe Kwamandan Iran da kona tutar Amurka

Mambobin Kungiyar Shi’a a Najeriya IMN, sun yin zanga-zanga a Abuja saboda kisan da aka yi wa babban Kwamandan Iran Qassem Soleimani. Mabiya shi’an sun bukaci gwamnati ta saki jagoran kungiyar Sheikh Ibrahim Elzakzaky, da ya kwashe shekara hudu a hannun hukuma da matarsa Zeenat. Masu zanga-zangar suna rike da kwalaye da suke kone da […]

An yi zanga-zangar kashe Kwamandan Iran da kona tutar Amurka

Mambobin Kungiyar Shi’a a Najeriya IMN, sun yin zanga-zanga a Abuja saboda kisan da aka yi wa babban Kwamandan Iran Qassem Soleimani.

Mabiya shi’an sun bukaci gwamnati ta saki jagoran kungiyar Sheikh Ibrahim Elzakzaky, da ya kwashe shekara hudu a hannun hukuma da matarsa Zeenat.

Masu zanga-zangar suna rike da kwalaye da suke kone da tutar Amurka don nuna fushinsu ga kisan da aka yi wa babban Kwamandan Iran, kuma sun yi Allah wadai da matakin Amurka.