An yi zanga-zangar kin jinin Majalisar dinkin Duniya a Juba

Mutane fiye da dubu ne suka yi zanga-zanga ranar Litinin da ta gabata a garin Juba da ke Sudan ta Kudu akan zargin da suke wa Majalisar dinkin Duniya na taimakawa ‘yan tawaye kasar da makamai. Ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta kama wasu makamai a cikin ayarin motocin […]

An yi zanga-zangar kin jinin Majalisar dinkin Duniya a Juba

Mutane fiye da dubu ne suka yi zanga-zanga ranar Litinin da ta gabata a garin Juba da ke Sudan ta Kudu akan zargin da suke wa Majalisar dinkin Duniya na taimakawa ‘yan tawaye kasar da makamai.
Ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta bayyana cewa ta kama wasu makamai a cikin ayarin motocin Majalisar dinkin Duniya wanda da fari aka ce abinci suke dauke da shi.
Majalisar dinkin Duniyan wadda ke da dakaru fiye da dubu takwas a kasar ta musanta zargin, sai dai kuma ta ba da hakuri ne kan kuskuranta na hucewa da makaman ta kasa. Ta ce makaman wanda za a rabawa sojojin Ghana ne wadan da ba su jima da isa kasar ba don aikin kiyaye zaman lafiya. Masu zanga-zangar dai suntan kiraye-kirayen murabus din Jakadiyar Mussaman ta Majalisar dinkin Duniya a Sudan ta Kudu wato Hilda Johnson.
Dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu sun kama makaman ne a garin Rumbek a hanyar su ta isa garin Bentiu, babban birnin Jihar Unity.
Mai Magana da yawun Majalisar dinkin Duniya, Ariane kuentier  ya shaida wa shirin turanci na BBC Focus on Africa cewa  za a turo da ayarin da za su  yi aiki tare da gwamnatin Sudan ta Kudu don gudanar da cikakken bincike kan al’amarin. Ya kuma kara da cewa al’amarin na da ban takaici matuka, saboda yadda wasu za su ba shi mummunar fahimta.
A watan Disambar bara ne dai fada ya barke tsakanin dakarun da ke biyayya da Shugaban kasa Salba Kiir da wanda ke goyon bayan mataimakinsa Riek Machar wanda hakan ya tilassawa mutane fiye da dubu dari takwas barin gidajensu. Za dai a ci gaba da tattaunawar maido da zaman lafiya wadda ake yi a kasar Habasha ranar Alhamis mai zuwa.