An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina
A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun […]

A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi.
Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun tsayar da su domin tuhuma bisa zargin cewa masu yi wa ’yan bindigar daji leƙen asiri ne.
Wannan harbin da suka yi ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi mai suna Saidu Abdulkadir.
Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya an kama wani ɗalibin jami’ar yana safarar makamai.
Bayanai sun ce hakan ne ya sanya wasu ke tunanin ’yan bijilantin sun yi amfani da wancan lamari da ya faru har suka aikata abin da ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi a yanzu.
Dangane da hakan ne ɗaliban ke zanga-zangar neman a gudanar da bincike tare gurfanar da waɗanda suka yi wannan kisa hukuncin da ya dace don tabbatar da adalci.
Kakakin rundunar ’yan sandan Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar hakan kuma ya ce suna kan binciken lamarin.
